✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Tinubu nake so ya gaji Buhari – El-Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-rufa’i ya ce jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu yake goyon baya a matsayin dan takarar Shugaban Kasa na…

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-rufa’i ya ce jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu yake goyon baya a matsayin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a dandalin Murtala Square da ke Kaduna, inda tsohon Gwamnan na Legas kuma mai neman takarar a APC ya gudanar da gangamin neman amincewar daliget din Jihar ranar Laraba.

Gangamin dai ya sami halartar tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cim Hanci da Rashawa ta EFCC, Malam Nuhu Ribadu da tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

Tun da farko dai Sanata Shettima ya ba daliget din tabbacin cewa Gwamna El-rufa’i na tare da su 100 bisa 100.

Sai dai lokacin da yake nasa jawabin, El-rufa’i ya ce dole yana bukatar hadin kan daliget din kafin hakarsa ta kai ga cim ma ruwa.

Ya ce yana tare da Tinubu bil-hakki, ko da yake ba zai yanke shawara ba tare da jin ta bakin daliget din ba, a matsayinsu na masu ruwa da tsaki.

“Kafin na tabbatar da abin da Sanata Kashim Shettima ya fada, ina so in fara tabbatar wa ta hanyar ji daga bakin daliget dinmu, shin kuna tare da Bola Tinubu?,” inji El-rufa’i, inda suka amsa da murya daya suka ce eh.

 

“Ranka ya dade yadda suka fada min haka nake yi, su ne iyayen gidana. Mu a APCn Jihar Kaduna haka muke yi,” inji shi.