Bisa ga dukkan alamu dai, ’yan takarar Gwamna biyu ne suka bayyana a jam’iyyar PDP ta Jihar Kano bayan kammala zaben fid da gwanin da tsagin jam’iyyar suka shirya a wurare daban-daban.
Aminiya ta rawaito cewa kowanne tsagi daga cikin bangarorin da ba sa ga maciji da juna na Shehu Wada Sagagi da na Aminu Wali, ya gabatar da zaben na shi.
- Zaben fid da gwanin PDP: Daliget 2 ne suka zabi Shehu Sani a Kaduna
- Zargin batanci: Rashin lafiyar Alkali ta janyo tsaiko a shari’ar Sheikh Abduljabbar
Sakamakon zaben tsagin Sagagi dai, wanda shi ne a farkon makon nan kotu ta tabbatar da sahihancinsa, ya zabi dan tsohon Shugaban mulkin soja na Najeriya, Muhammad Abacha, a matsayin dan takara.
Shi kuwa daya tsagin ya ayyana Muhammad Sadiq Wali, da ga tsohon Ministan Harkokin Waje, Aminu Wali ya lashe.
Baturiyar zaben tsagin Shehu Sagagi, Amina Garba, ta ce ya samu nasarar ne ranar Laraba da kuria 736 a zaben fid da gwani na jam’iyyar.
Shugaban kwamitin zaben jam’iyyar, Alhaji Muhammad Jamu ya ce zaben an yi shi ne ta halastacciyar hanya da ingantattun daliget, da kuma sahalewar hukumar zabe, jami’an ’yan sanda, da rundunar tsaro ta farin kaya.
Shi kuwa tsagin Ambasada Aminu Wali da Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya jagoranta, sakamakon ya nuna Sadiq Wali ya samu nasara ne da kuri’a 455, sai mai biye masa Ali Amin Little da ya samu kuri’a 333.
Shugaban kwamitin zaben Bunmi Adu ya tabbatarwa Sadiq Wali a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar.
Sauran wadanda ya gwabza da su sun hada da tsohon shugaban ma’aikata Dokta Yunusa Adamu Dangwani, da Dokta Yusuf Bello Dambatta wanda ya taba rike Kwmishinan Kasa da Safayo da ya samu 182.
Tsohon Kwamishinan Ganduje, Mu’az Magaji ya samu kuri’a 25, sai Mustapha Bala Getso mai 20, da Muhuyi Magaji mai 25.
To sai dai Magaji tun da fari ya janye takararsa ta gwamna domin fafatawa da shi a kujerar Sanatan Kano ta Arewa.
Mutane shida ne dai suka yi takara a tsagin na Aminu Wali, sai biyu wato Jafar Sani Bello da Muhammad Abacha da suka kara a tsagin Sagagi.
Masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin cewa rikicin na iya yi wa jam’iyyar mummunar illa a zabe mai zuwa.