Shugaban Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), Baffa Babba Dan-Agundi, ya ce Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya ki amincewa da bukatarsa ta ajiye aiki.
A kwanan nan ne dai Baffan ya aike wa Gwamnan takardar neman ajiye aikinsa don yin takara a zaben shekarar 2023 da ke tafe, kamar yadda Dokar Zabe ta tanada.
- Yadda nasiha ta jawo wa matashi rasa hannu daya a Kano
- Ina shekara 3 na haddace Kur’ani —Dan shekara 8 mai Tafsiri
Sai dai da yake magana da wakilinmu, Shugaban na KAROTA ya tabbatar da cewa ya mika takardar ajiye aiki a ranar Litinin, amma hakarsa ba ta cim ma ruwa ba.
“Tabbas na mika wannan takarda amma Gwamna ya ce na dakata tukunna.
“Gwamna kamar uba yake a wajena, domin haka, ba zan bijirewa bukata ko umarninsa ba,” inji shi.
Ya kara da cewa shi mai biyayya ne ga umarnin Gwamnan a matsayinsa na wanda ya taimaka mishi wajen cim ma nasarori a rayuwa.
Tun farko dai sakamakon kin amincewa da takardar ajiye aikin ya fito ne ta hannun Mukaddashin Gwamnan Jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, bisa umarnin Gwamna Ganduje a halin yanzu yake birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ana ganin Baffa Babba Dan-Agundi dai a matsayin daya daga cikin na hannun daman Gwamna Ganduje a Kano.