✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

14 ga Janairu za a fara gasar firimiyar Najeriya

Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce ta ware ranar 14 ga Janairun, 2018 a matsayin ranar da za a fara gasar rukuni-rukuni…

Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce ta ware ranar 14 ga Janairun, 2018 a matsayin ranar da za a fara gasar rukuni-rukuni ta kasa wato firimiya.

Sai dai kafin wannan lokaci, Kwamitin da ke kula da yadda gasar ke gudana (League Management Company, LMC) zai yi taron na musamman daga ranar 11 zuwa 17  ga watan Disambar 2017 don tattauna batutuwa da suka shafi gasar kamar yadda ake yi duk shekara.

Daga cikin batutuwan da Kwamitin zai tattauna sun hada da na kulob hudu da suka samu shiga gasar daga rukunin ’yan dagaji (amateur) inda za a fadakar da su ka’idojin da yakamata su cika kafin a fara da kuma yayin gasar musamman a bangaren biyan ’yan kwallonsu da na jami’ansu albashi da alawus-alawus da batun sanya hannu a kwantaragi da kuma batun saye da sayar da ’yan kwallo.

Haka kuma NFF ta ce za ta gudanar da taron shekara-shekara (AGM) a Jihar Kano  a ranar 16 ga watan Disambar 2017 don tattauna muhimman batutuwa da suka shafi hukumar da kuma harkar kwallon kafa a kasa baki daya.

Salihu Abubakar, Shugaban Kwamitin LMC ya ce a yayin taron ne za a fitar da jadawalin yadda gasar firimiya ta bana za ta kasance. Sauran batutuwan sun hada da yin bincike don gano ko kungiyoyin da za su fafata a gasar sun cika ka’idojin shiga gasar da suka hada da biyan ’yan wasa da jami’ansu hakkokinsu a kan lokaci da kuma duba halayen da filayen wasannin kungiyoyin suke ciki kafin  a fara gasar da sauransu.

Hukumar NFF ta ce ta kebe ranar 5 ga watan Janairun 2018 a matsayin rana ta karshe da aka dibarwa kungiyoyin da su kasance sun cika su kafin a fara gudanar da gasar, in ba haka ba za a dauki matakin dagewa daga duk kungiyar da ba ta cika wadannan ka’idojin ba.