✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: Saudiyya ta ninka harajin kaya sau uku don rage asara

Kasar Saudiyya za ta kara harajin kaya (VAT) daga kashi biyar zuwa 15 cikin 100 a watan Yuli. Ma’aikatar kudi ta kasar ce ta sanar…

Kasar Saudiyya za ta kara harajin kaya (VAT) daga kashi biyar zuwa 15 cikin 100 a watan Yuli.

Ma’aikatar kudi ta kasar ce ta sanar da ninka kudin harajin kayan sau uku a wani mataki na tallaa wa tattalin arzikin kasar yayin da ake fafutuka da annobar coronavirus.

A watan Yuni Masarautar Saudiyya za ta dakatar da bayar da kudin alawus na tsadar rayuwa.

Shekara biyu da suka wuce ne Sarki Salman ya ba da umarnin a rika ba da alawus din ga ma’aikatan gwamnati da na rundunonin soji.

Ministan kudi na kasar Mohammed al-Jadaan, ya ce wannan annobar ta jawo raguwa a kudaden shigar da ake samu, hakan ya sa dole gwamnati ta rage kudaden da take kashewa sannan ta kirkiro da hanyoyin samun kudi da ba na man fetur ba.

“Daukar wannan matakin ba zai yi wa ’yan kasar dadi ba, amma ya zama dole,” inji Mohammed al-Jadaan.

Masarautar za ta kuma rage wasu kudade da aka ware don aiwatar da wasu ayyuka da suka shafi Muradun 2030, wani gagarumin shirin Yarima Mohammed bin Salman na fadada hanyoyin samun kudin shiga.

Saudiyya ce ta fi ko wacce kasar Larabawa yawan wadanda suka kamu da coronavirus, inda rahotanni suka tabbatar da mutum 39,000 ne suka kamu, yayin da mutum 246 suka riga mu gidan gaskiya.

Tun bayan bullar cutar a watan Maris kasar Saudiyya ta dauki matakan kariya na hana yaduwar cutar, inda ta sanar da dokar hana fita a wasu manyan biranen kasar tare da ziyartar kasar don gudanar da ibadada kuma dakatar sufurin jirage kasashen waje da na cikin gida.

Tuni aka sanar da wani tallafi na kudin kasar riyal biliyan 120 daidai da dalar Amurka biliyan 32 don taimakawa ”yan kasuwar da annobar ta shafa.