✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗan Najeriya na yunkurin kafa tarihin yin maganar awa 120 babu tsayawa

Yana kokarin kwace kambun awa 90 daga hannun wani dan kasar Nepal

Wani matashi mai suna Christopher Olusa, ya ce ya shirya tsaf domin rike kundin bajinta na Guinness ta hanyar yin magana ta tsawon awa 120 babu tsayawa.

Matashin, wanda dalibi ne da ke karatun digirinsa na biyu a Jami’ar Fasaha ta Akure (FUTA) da ke Jihar Ondo ya ce yana so ya yi amfani da shiga bajintar wajen karfafa gwiwar matasa don ciyar da kasa gaba.

Yana dai kokarin kwace kambun da wani dan kasar Nepal mai suna Ananta Ram ke rike da shi ne na tsawon awa 90 da minti biyu a shekara ta 2018.

Amanta dai ya fara magana ne da misalin karfe 6:15 na safiyar 27 ga watan Agustan 2018 sannan ya gama da karfe 12:17 na safiyar 31 ga watan Agusta.

Mai rike da kambun dai kafin ya shafe kusan kwana bakwai kafin ya ce uffan a shirye-shiryen fara gasar a lokacin.

To sai dai Christopher ya ce yana so ya kafa tarihin yin maganar ta kwana biyar da zai fara daga ranar 11 ga watan Satumban 2023 a otel ɗin Dejavu da ke Akure.

Matashin, wanda ya yi jawabi ga manema labarai ranar Alhamis a Akure, ya ce tuni ya samu amincewar kundin na Guinness domin shiga gasar.

Ya yi bayanin cewa sai da ya yi gwaji na tsawon lokaci a baya kafin ya yi yunkurin shiga gasar.