✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗan bindiga ya sanya wa manoma haraji a ƙauyukan Katsina

Dan bindigar dai shi ne ya addabi Batsari, Safana da Ɗanmusa

Wani ƙasurgumin ɗan bindigar daji da ya addabi yankunan Batsari, Safana da Ɗanmusa a Jihar Katsina, ya sanya wa wasu ƙauyukan yankin harajin riɗin da suka noma kafin ya bar su su kwashe abin da suka noma.

Ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Usman Moɗi-moɗi wanda ya addabi yankin ne ya sa harajin ga manoman yankin.

Aminiya ta gano cewa ɗan bindigar ya nemi duk manomin da ya noma riɗi dole ya fitar masa da wani kaso a matsayin haraji.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, “Dole mazauna wadannan yankuna su rika bin duk wani umarnin da ’yan bindigar suka ba su don su zauna lafiya.

“Kauyuka irin su Habul, Goni, Gobirawa, Guzurawa, Kunkunna, Makera, Tsaskiya har zuwa irin su Ummabadau ba su da yadda za su yi saboda babu wani tallafi ko gudunmuwar da za a iya kai musu.

“Har ila yau, kauyukan Ganye, Ba Dole, Sabuwar Bugaje, Alhazawa da sauran duk wani kauyen da ke bakin dazuzzukan da barayin nan suke ba su da zabi, dole su bi.”

Majiyar ta kuma ce duk da akwai sansanin sojoji a garin Runka da ke yankin, amma ba za su iya shiga yankunan ba, saboda mota ba ta shiga, su kuma ba su da babura.

Kazalika, ya ce ba zai yiwu sojojin su shiga yankunan a kasa ba, saboda ana yi musu kwanton bauna a kai musu hari, sannan akwai masu ba ’yan bindiga bayanai a kansu.

Bugu da kari, Aminiya ta nemi karin haske daga bakin wani manomin da ya ce lamarin ya shafe shi kai tsaye kuma ya biya nasa harajin.

“Wanda bai noma riɗin ba kuma suna amsar kuɗi a maimakon shi, abin da ya fara daga dubu ɗaya zuwa sama.

“Wani abin takaicin kamar yadda muka samu rahoto shi ne, baya ga biyan harajin, wasu manoman ma an hana su ɗibar amfanin gonar yayin da ake tare wasu a hanya a kwace a lokacin da za su kai kasuwa su sayar.

Usman Moɗi-moɗi, idan za a iya tunawa shi ne a baya ake zargi da kisan ’yan sandan dake Karamar Hukumar Dutsinma.

Har ila yau, shi ne jagoran ’yan fashin dajin da ke satar shanu, garkuwa da mutane tare da sauran duk wasu ayyukan ta’addanci a yankin.