✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya kaddamar da fara gina gadar sama ta biyu a Borno 

Za a gina gadar ce a kan kudi Naira biliyan 5.8

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da aikin gina gadar sama ta biyu a mahadar Borno Express a babban birnin Jihar, Maiduguri.

Idan dai za a iya tunawa, Gwamna Zulum ya gina gadar sama ta farko a Borno a Unguwar Kwastam da ke Kasuwar Gamboru, wacce kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a watan Disamba 2021.

Gadar ta biyun dai za ta kewaya babban titin Borno Express wanda ke da tashar T-junction, tare da hanyoyin da suka hada muhimman sassa uku na Maiduguri zuwa filin jirgin sama na kasa da kasa, filin wasa na garin da Tashan Kano, da kuma tsakiyar birnin dab da sakatariyar Jihar da ke jikin gidan waya (Post Office,) da kasuwar Monday Market,  da sauransu.

Yayin kaddamar da aikin, Gwamna Zulum ya tabbatar wa ’yan kwangilar cewa, “Insha Allahu, mu Gwamnatin Jihar Borno za mu tabbatar da sakin kudaden kamar yadda ya kamata.

“Ina kuma ba ku shawarar ku tabbatar kun gudanar da aiki mai inganci kuma In sha Allahu wannan mataki ne na gaba na ciyar da rayuwar al’ummar gaba. Za mu samar da karin romon Dimokuradiyya ga al’ummar Borno,” Gwamnan.

Wani kamfanin kasar China mai suna EEC ne aka ba kwangilar aikin ginin gadar a kan kudi Naira biliyan 5.8.

Kwamishinan ayyuka na Jihar, Isa Garba Haladu ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar kwangilar a madadin gwamnatin Jihar yayin da wakilin kamfanin na EEC ya rattaba hannu a madadin kamfanin na kasar Sin.

Gwamnan ya ba kamfanin wa’adin karshen wannan shekara ta 2023 domin ya kammala aikin.