✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zazzabin Lassa: Ta kashe183, wasu 1028 sun harbu a Najeriya

NCDC ta ce har yanzu ba a samu ma'aikacin lafiya da ya harbu da cutar ba.

Mutum 183 sun rasu sakamakon kamuwa da Zazzabin Lassa a Najeriya, inda mutum 1,028 suka harbu da cutar.

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) ta ce wadanda suka harbu da cutar sun fito ne daga kananan hukumomi 110 a jihohi 27, baya ga sabbin wadanda suka kamu da ita a jihohin Bauchi, Ondo, Ebonyi da Sakkwato.

Rahoton hukumar na mako 49 ya ce, “Adadin wadanda suka kamu da cutar Zazzabin Lassa ya karu idan aka kwatanta da rahoton 2021.

“Sai dai kawo yanzu ba a samu ma’aikacin lafiya da ya harbu da ita ba kuma suna ci gaba da aiki a jihohi don ganin an ceto mutane daga kamuwa da ita.

“Kuma yana da kyau mutane su ci gaba da bin matakan kariya da kaurace wa shiga cunkoso idan ba ya zama dole ba.

“Da zarar an ji wani yanayi da ba a saba ji ba a garzaya zuwa asibiti ko cibiyoyin lafiya don yin gwaji,” in ji rahoton.

Zazzabin Lassa cuta ce mai hatsarin gaske, wadda ake daukar ta hanyar cudanya da mai dauke da ita kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana.

An fi samun cutar a kasashen Afrika kamar su Benin, Najeriya, Kamaru, Ghana, Laberiya, Mali, Saliyo da sauransu.