✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan dauki mataki kan masu amfani da addini su tayar da rikici —Gwamna

Gwamnan Jihar Taraba Darius Ishaku ya yi barazanar sanya kafar wando da malaman addini da ya zarga da hura wutar rikici a jihar. Kashedin nasa…

Gwamnan Jihar Taraba Darius Ishaku ya yi barazanar sanya kafar wando da malaman addini da ya zarga da hura wutar rikici a jihar.

Kashedin nasa na zuwa ne yayin da hare-hare da kuma daukar fansa musamman tsakanin ‘yan kabilar Jukun da makwabtansu ‘yan kabilar Tibi ya ki ci, ya ki cinyewa a jihar.

Darius Ishaku ya koka cewa wasu limaman addini da ya kamata su yi kira a zauna lafiya suke tunzura jama’a, yana mai cewa ba zai raga wa duk mai yin cikas ga kokarin wanzar da zaman lafiya a jihar ba.

“Ni da takwarana Gwaman Samuel Ortom muna kai-komo a Binuwai da Taraba domin samun zaman lafiya amma kaico! Wasu limaman addini na mana kafar ungulu.

“Ba zan lamunta ba domin aikina ne a matsayin gwamna in samar da dawwamammen zaman lafiya”, inji shi.

A bayaninsa yayin karbar bakuncin Kwamitin ‘Yan Gudun Hijira ‘Yan Kabilar Tibi a Jihar, gwamnan ya nuna damuwa kan halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki, tare da yin kira ga jama’a su bayar da hadin kai zaman lafiya ya dore a jihar.

“Taraba jiha ce mai addinai da kabilu da yawa inda za ka samu ‘yan uwa da surukai kowannensu bangaren da ya fito daban. Saboda haka abin da ya fi dacewa shi ne mu rungumi juna mu zauna lafiya”, inji gwamnan.

Ya kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya a cikin al’umma wanda ya ce sai da shi ake samun kwanciyar hankalin da ke bayar da damar samun ci gaba.