✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan bi diddigin kisan da aka yi wa Hanifa —Shekarau

Da kaina zan bi diddigin lamarin har zuwa karshensa.

Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya sha alwashin cewa da kansa zai ci gaba da bin diddigin kisan gillar da aka yi wa wata yarinya ’yar shekara biyar a Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa, Hanifa Abubakar ’yar shekaru biyar da malamin makarantarsu ya yi garkuwa da ita, ya kuma kashe ta, tuni ya shiga hannu kuma bincike a kan lamarin ya kankama.

Sai dai a wani sako da ya aike wa iyaye da ’yan uwanta, Sanata Shekarau ya ce zai bi diddigin lamarin domin ganin an bi mata hakkinta.

Tsohon Gwamnan ya bayyana cewa bai kamata a yi kisan kai irin wannan ba kuma a zuba ido ba tare da an dauki mataki cikin gaggawa ba, yana mai shan alwashin bin diddigin lamarin har zuwa karshensa.

Sanata Shekarau ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya bai wa iyalan marigayiyar hakurin jure rashin da suka yi.

Tuni dai rahotanni suka bulla cewa an kama malamin makarantar Abdulmalik Tanko wanda magidanci ne da ke da kananan yara uku, da kuma sauran mutane biyu da ake kyautata zaton suna da hannu a lamarin da suka hada da wata mace.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ba da umarnin rufe makarantar da Hanifa ta ke zuwa kafin gamuwa da ajalinta, inda kuma malamin ya binne ta kafin hukuma ta tono gawarta.

Kasa da mako guda bayan kama malamin da kuma tono gawar Hanifa, matasa suka huce fushin kisanta wajen cinna wa makarantar wuta, duk da yake hayar ginin mai makarantar, Abdulmalik Tanko ya ke yi.

Kazalika, Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci hukumomin ’yan sanda da na ma’aikatar shari’a da su tabbatar da yin adalci wajen aiwatar da hukunci kan kisan da aka yi wa Hanifa.