✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamfara ta lashe Gasar Al-Kur’ani ta Kasa

Zamfara ta lashe rukunin Izu 60 da Tafsiri, Kano kuma Izu 60 da Tajwidi

Mahaddatan Al-Kur’ani daga Jihohin Zamfara da Kano sun dauki kambin Gasar Musabakar Al-Kur’ani ta Kasa karo na 35 da aka kammala a Kano.

Gwarzon Shekarar na gaba daya a musabakar shi ne Muhammad Auwal Gusau daga Jihar Zamfara, wanda ya doke sauran abokan karawarsa a rukunin haddar Izu 60 da Tajwidi da Tafsiri.

Bayan bayyana shi, an nada masa rawani a matsayin gangaran, mahaddacin Al-Kur’an na kololuwa, bisa al’adar musabakar.

Mahaddaciyar da ta zama Gwarzuwar Shekara, a bangaren mata na Izu 60  ita ce Nusaiba Shuaibu Ahmad daga Jihar Kano.

Maddatan Al-Kur’ani fiye 300 ne suka fafata a tsakaninsu a tsawon mako guda a musabakar wadda kuma aka kammala a ranar Asabar, 27 ga Maris, 2021.

Alkalan musabakar a ranar rufewa

Kwamitin Alkalai mai mutum bakwai ne ya rika bin kwakkwafi a yayin da kowanne daga cikin mahaddatan yake karatu a bisa mum bari.

Ayyukan alkalan sun hada ta jan baki, bibiyar yadda mahaddaci ke cika ka’idojin Tajwidi a yayin karatu, karfin hadda, nutsuwa da sauransu.

Kowanne bangare an ware masa alkali mai sa ido tare da ba da maki a kansa daga cikin alkalai shida da ke aiki a lokaci guda yayin da daya ke zaman jiran ko-ta-kwana.

Wani sashe na ‘yan kwallo a lokacin musabakar

Rukuni shida da ne aka fafata a musabakar da suka hada da Izu 60 ta Tajwidi da Tafsiri, Izu 60 da Tawjidi, Izu 40, Izu 20, Izu 10 sai kuma Izu biyu.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Babban Limamin Masallacin Kasa, Farfesa Shehu Ahmad Sa’id Galadanci, manyan malamai, alarammomi, da sarakakuna da dama sun halarci taron rufewar.

Musabakar da ta samu wakilici daga jihohin Najeriya ta kuma samu halarcin mutane daga sassan Najeriya.