Na ji ana cewa a kiyayi zaki da maiko. To shin ba su da amfani ne ga jiki ko kuwa sai idan sun yi yawa ne suke zama matsala. Sa’annan wane irin abinci mai basur mai zubar da jini zai rika ci?
Daga Uwargida Amina
Amsa: Eh, kwarai kin kusa gano batun. Zaki da maiko suna da amfani a jiki. Sai zaki da maiko sun yi yawa a jiki ne yake zama illa.Wato abin ne yana da ’yar sarkakiya; idan ba ka ci ba, akwai matsala, idan ka ci da yawa ma akwai matsala, ke nan sai an daidaita su. A kimiyyance komai ana son sa saisa-saisa ne har zaki da maiko; idan suka yi kadan jiki yakan bukace su, idan kuma suka yi yawa nan ma dai jiki zai yaki yawan, dole sai mutum ya gano yadda zai saisaita su don lafiyar jikinsa.
Yawanci dabarar da likitanci ya kawo mai sauki ta saisaitawar ita ce – a ci daidai misali, amma a biyo bayan cin da kona su ta hanyar motsa jiki gami da cin kayan ganye da na itatuwa. Wato idan aka ci, jiki ya tsotsi abin da yake bukata to sauran ajiye su zai yi. Idan kina so kada jikinki ya ajiye su sai dai ki kona su ta hanyoyin da aka fada. Domin wannan ajiyar ce sanadiyar cututtukan zamani irin su kiba da hawan jini da ciwon suga da na sanyin kashi da sauransu. Idan da za a lura lafiyar
- Mutum mai cin zaki da maiko wanda ba ya kona su ba daya take da;
- Mutum mai ci mai kona ragowar ba. Haka nan lafiyar wannan na biyun ba daya take da;
- Mutumin da ba ya cin zaki da maiko kwata-kwata ba.
Kin ga ke nan an kasa mutane kashi uku ta bangaren cin zaki da maiko. Idan da zan zabi wanda zai fi lafiya a cikinsu, mutum na biyun zan zaba. Idan dai mutum ya kasance a aji na biyu to ba sai ya nemi wani maganin zaki da maiko na asibiti ba, ballantana wanda akan ji ana yawan talla a titi.
Sai amsar abincin mai basur. Basur mai zubar da jini mun sha fada a nan cewa watakila tiyata yake bukata ba wani nau’in abinci ba.
Idan na ci gyada sai in samu kuraje a fuska. Ko hakan na nufin ina da matsala ce?
Daga Abba H.
Amsa: Eh, kuma a’a. Gyada za ta iya kara maka maikon fuska, wanda hakan kan sa samari yawan kuraje a fuska. Wato samari (da ma wadansu ’yan mata) idan suka fiya cin gyada da abubuwa masu maiko sosai, kamar soyayyun abinci, sukan jawo musu kurajen fuska na pimples. Don haka sai ka kiyaye ka rika cin gyadar da kayan maiko saisa-saisa ko ka ci karago. Wadansu ma sai sun tsane maikon soyayyen abinci sukan iya ci domin ko yaya suka ci washegari sai katon kurji ya fito.
Wai shin ana allura a kirji ne? Na gani a fim an yi kuma an caka ta da karfi.
Daga Isa M
Amsa: Eh, ana allura a kirji amma ba kamar yadda sukan nuna a fim ba, a cikin nutsuwa da saiti ake yi. Yawanci allurai ne wadanda ake so maganin ya shiga cikin zuciya kai-tsaye.
Me ya sa idan ana goga karfe da karfe tsikar jikina take tashi in ji ba na so?
Daga Rabi’u Dangida, Zamfara
Amsa: Eh, ba kai kadai ba yawancin mutane (kashi 90 cikin 100) bincike ya nuna ba sa son irin wannan karar, saboda tana daga cikin nau’o’in kara wadanda kwakwalwa ba ta so, domin suna kama da kara masu ta da hankali kamar kukan jarirai, ko masu ban tsoro kamar ta ihun mace misali. Wannan tsikar jikin ai jijiyoyin laka ne nakan fata ke mimmikewa bayan kunne ya aika wa sashen kwakwalwa mai kula da sauti irin wannan karar. Idan kwakwalwar ba ta so duk sai lakar fatar jiki sun amsa sun nuna rashin jin dadinsu.
Matata ce aka yi wa gwajin ciwon hanta na hepatitis sai aka ga tana da shi. Ni kuma tun kafin mu yi aure an taba gwada ni ba ni da ciwon. Ko ni ma zan iya dauka?
Daga Mai Damuwa
Amsa: Kwarai kuwa za ka iya dauka amma abin farin cikin shi ne cewa za ka iya kare kanka in dai har ba ka riga ka dauka ba. Wannan hanya kuwa ita ce ta yin allurar rigakafin ciwon hantar na hepatitis. Don haka sai ka je inda aka yi mata awon a duba ka a ga abin da za a yi.
Idan na kwanta da dare na yi barci na tashi sai in ji bakina da harcena duk sun bushe.
Daga Majidadi Kano
Amsa: Watakila bakin ne kake barinsa bude a lokacin barcin har ya bushe sosai. Yawanci wannan na faruwa idan a busasshen yanayi ne, amma da damuna lokacin danshi mutum ko ya kwana baki bude zai wahala ya bushe. Ban da yanayi mura ma takan iya sa irin wannan.
Shin idan mutum ya fara manyanta sosai ya kamata ya rika zubar da majina a kai-a kai? Domin ni idan na fita ba hula a kaina sai na yi ta mura da zubar da majina amma idan na sa hula sai abin ya lafa
Daga Aminu Fagge
Amsa: Eh, ka san mura iri biyu ce, da wadda kwayoyin cuta na birus ke kawowa, da wadda canjin yanayi kan kawo. Canjin yanayi irin busasshen nan mai dan sanyi ya fi kawo mura. Kuma shi sanyin yakan iya shiga jiki ta wurare da dama; ta kai, ta kirji, ko ta kafa. Sa’annan kamar yadda ka fada yawan shekaru za su iya sa mutum yawan mura, saboda raunin garkuwar jiki. Don haka sai ka ci gaba da amfani da wannan kariya da ka gano, har yanayi ya canja ko har kwayoyin cutar su lafa ko kuma har lokacin da garkuwar jikin za ta kara kwari
Ni kuma idan rana ta dake ni sai kaina ya fara ciwo. Ko yawan shiga rana zai iya illa ga lafiyata?
Daga Musa GGC Kano
Amsa: Kwarai kuwa yawan shiga rana zai iya illa ga lafiyarka. Wannan ciwon kai da kake ji ai kwakwalwa ce take maka nuni cewa ka fita daga ranar haka, kana ba ta wahala, wato kana kona ta. Idan ma abin ya yi yawa ai aikin kwakwalwar zai iya dan tsayawa a samu abin da muke kira heat stroke, wato bugun rana, mutum kawai ya ji ya yanke jiki ya fadi ya suma, sai kwakwalwar ta yi sanyi ya farfado. Ai za ka ga abokan zamanmu sauran kabilu a lokacin da ake rana ba sa yarda su fito sai rana ta lafa ko kuma idan ta kama dole a fito cikin rana, sai su nemi lema su yi amfani da ita.