Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Zaki da bera.’ Labarin na kunshe da darussa da dama kamar na taimaka wa dan uwa don ba a san abin da gobe za ta haifar ba.
Akwai wani Zaki a wani daji da ake kira da suna ‘dam’. Bayan Zaki ya ci, ya koshi sai barci mai nauyi ya kwashe shi a karkashin wata bishiya. Can sai ga bera yana wasa a kan Zaki. Zaki sai ya ji kamar ana wasa a kansa. Sai ya farka don ya ga abin da ya tada shi daga barci sai ya yi ido hudu da bera.
Bera ya razana ya gigice. Zaki ya ce sai ya kashe shi. Sai bera ya ba shi hakuri. Kamar zaki zai kashe shi, sai ya hakura.
Wata ran a bera zai wuce sai ya hango zaki a kame a tarkon wani maharbi. Nan take Bera ya sa hakoransa ya tsittsinke tarkon sannan Zaki ya kubuta.
Tun daga ranar aka kulla abota a tsakanin Zaki da Bera.
Manyan Gobe kun ga da Zaki bai hakura ba a wancan lokaci ya kashe bera da shi ma bai samu kubuta a wannan lokaci ba.
Da fatan Manyan Gobe za su yi shagulgulan Sallah lafiya.