✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaftarewar kasa ta kashe mutum 23 a Indiya

Baraguzan gini sun kashe mutum 17 ’yan gida daya a birnin Mumbai.

Akalla mutum 23 ne suka rasu bayan faduwar wata katanga a kansu sakamakon zaftarewar kasa da aka samu bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a Mumbai, babban birnin kasuwanci na kasar Indiya.

Hukumar Kula da Bala’o’i ta Kasar (NDRF) ta ce kusan daukacin mazauna gidan ne suka rasu bayan faduwar bishiyar da ta rusa katangar a gabashin unguwar Chembur a safiyar ranar Lahadi.

  1. Akwai yarjejeniyar Buhari zai mika mulki ga Tinubu a 2023 —Sanata Hanga
  2. Sau nawa aka taba soke gudanar da Aikin Hajji a tarihi?

Hukumar ta ce an gano gawarwaki 17 daga cikin baraguzan ginin, a yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

“A gidan da ke makwabtaka da shi kuma na ga wata karamar yarinya da baraguzan gini suka danne, tana ihu tana cewa ‘ku cece ni, ku cece ni’.

“Jikinta ya makale a cikin laka, da kyar na iya ciro ta, amma ta samu raunuka a kafafunta. Ni ma da kyar na tsira daga rushewar ginin,” inji Firoz Khan, wanda ya tsallake rijiya da baya a iftila’in.

Wata mazauniyar yankin, Manda Gautam Pradhan, ta ce ta ga “duwatsu da laka suna ta kwarara daga wani tsaunin tare da ruwan sama”.

NDRF ta ce wasu mutum shida sun rasu a unguwar Vikhroli da ke birnin bayan zaftarewar kasa da ta ritsa da gidaje biyar a safiyar Lahadi.

Ta ce ruwan saman ya mamaye wata matatar ruwa, wanda hakan ya kawo cikas ga samar da ruwan sha “a yawancin sassan birnin Mumbai”, mai mazauna miliyan 20.

Don haka ta shawarci mazauna da su rika tafasawa tare da tsaftace ruwa kafin su yi amfani da shi.

Tun ranar Asabar ake ta tafka ruwan saman da ya tsayar da ayyukan sufuri na cikin gida.

Ana yawan samun rushewar gine-gine a lokacin damina tsakanin watannin Yuni zuwa Satumba a Indiya, lamarin da ya fi shafar tsoffin gine-gine.

Ko a watan Yuni, mutum 12 sun mutu bayan wani gini ya rufta a wata unguwar marasa galihu a Mumbai.

A watan Satumbar bara, mutum 39 sun mutu sakamakon rushewar wani bene mai hawa uku a Bhiwandi da ke kusa da birnin.

A safiyar Lahadi Sashen Kula da Yanayin Sama na Indiya ya ce an yi hasashen “samun matsakaicin ruwan sama ko mai karfi ko kuma tsawa” a kwanaki biyu masu zuwa.

Firai Minista Narendra Modi ya aike da sakon ta’aziyyarsa tare da alkawarin biyan diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa.

%d bloggers like this: