✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Shugabannin APC ya bar baya da kura a Jihohi da dama

A Jihohi da dama dai shugabanni biyu sun bayyana, a wasu kuma aka fuskanci tarzoma.

Zabukan shugabannin jam’iyyar APC mai mulkin da aka gudanar ranar Asabar sun bar baya da kura a Jihohi da dama na Najeriya.

Ko da yake, a wasu Jihohin an yi amfani da sulhu wajen zaben ’yan takara, a wasu kuma da dama an samu baraka inda wasu suka yi ta ware suka gudanar da nasu tarukan a gefe.

Hakan dai baya rasa nasaba da yadda masu ido da kwalli a jam’iyyar suke gwajin kwanji wajen tabbatar da ikonsu da jam’iyyar, duk kuwa da yunkurin da kwamitin rikonta na kasa, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi wajen ganin ya dinke kan ’yan jam’iyyar gabanin zaben.

Ko a ranar Juma’a dai sai da Mai Mala ya yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar kan su kasance tsintsiya madaurinki daya, yana mai cewa sun yi kyakkyawan shiri wajen ganin an yi zaben lami lafiya.

An sami baraka a Jihohi da dama

To sai dai duk da irin wannan tabbacin na yin zaben cikin lumana da kuma gargadi ga masu yunkurin yin zagon kasa, an sami tarzoma a wasu Jihohin da dama.

A Jihar Kano alal misali, tsagin da ke karkashin tsohon Gwamnan Jihar, Malam Ibrahim Shekarau ya shirya nasa taron daban da na wanda ke biyayya ga Gwamna Abdullahi Ganduje.

Hakan dai ya sa sai da aka aike da jami’an tsaron ’yan sanda da na DSS suka tarwatsa ’yan tsagin na Shekarau sannan suka rufe wajen taron, kafin daga bisani su canza wani wajen na daban.

Daga bisani dai, bangaren Ganduje ya zabi Abdullahi Abbas a matsayin Shugaba, yayin da tsagin Sanata Shekarau ya Zabi Ahmadu Haruna Zago a matsayin nasa shugaban.]

Shugabanni 2 sun bulla a Neja da Imo da Osun da Akwa Ibom

A Jihar Neja ma haka lamarin yake, inda Shugabanni biyu suka bulla a Jihar tsakanin tsagin da ke biyayya ga Gwamna Abubakar Sani Bello da wadanda ke adawa da su.

A Imo ma haka lamarin yake, inda tsagin da ke biyayya ga tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rochas Okorocha ya kauracewa zaben da ya ayyana Dokta Macdonald Ebere a matsayin sabon Shugaban jam’iyyar.

Macdonald dai tsohon Mai Taimaka wa Gwamna Hope Uzodinma ne a Jihar.

An yi harbe-harbe a Osun

A Osun kuwa, akalla mutum biyu ne rahotanni suka tabbatar da an raunata a wata tarzoma da ta barke a wajen wani taron da tsagin jam’iyyar da ke biyayya ga Ministan Cikin Gida, Rauf Arebesola, ya shirya  a Oshogbo, babban birnin Jihar.

Jagoran tsagin dai, Mista Adelowo Adebiyi, ya zargi Gwamnan Jihar da daukar nauyin kai harin saboda ya razana mambobinsa.

A Oyo kuma, jam’iyyar ta sanar da dakatar da zaben ne har zuwa wani lokaci a nan gaba, a daidai lokacin da ake zargin an bugo takardun bogi don tafka magudi a zaben, kamar yadda a Taraba kuma fargabar tayar da zaune tsaye c eta sa aka dage zaben.

A Jihar Akwa Ibom ma ba ta sauya zane ba inda tsagin da ke biyayya ga Ministan Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio ya shirya nasa zaben, yayin da tsagin Sakataren APC na kasa, Sanata Akpan Udoedeghe shi ma ya shirya nasa daban.

Kazalika, sauran Jihohin da aka sami baraka a shirya taron sun hada da Legas da Enugu da Ogun da kuma Kwara.

An yi zabe lafiya a wasu Jihohin

Sai dai zaben ya gudana lami lafiya a Jihar Yobe, mahaifar Shugaban jam’iyyar na riko, kuma Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni, da kuma a Jihar Abiya.

A Edo kuwa, jami’an tsaro ne suka hana ’yan jarida shiga wajen taron, sai kuma a Jihohin Nasarawa da Gombe da Kaduna da Kuros Riba da aka zabi sabbin Shugabannin ta hanyar maslaha.

A wani mataki kuma mai kama da ba-saban-ba, a Jihar Jigawa, an zabi akalla mata bakwai daga cikin sabbin shugabannin APC a Jihar.