✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Ondo: Harbe-harbe na razana garin Akure

Hatsaniyar na zuwa ne mako guda kafin zaben gwamnan jihar Ondo da manyan jam’iyyu ke kokarin lashewa

Jama’ar garin Akure na Jihar Ondo sun wayi garin Lahadi  cikin firgici sakamakon karar harbe-harbe da ta cika garin.

Harbe-harbe da aka yi ta yi sun biyo bayan gwabzawa da aka yi tsakanin magoya bayan dan takarar gwamnan jihar na jam’iyya mai mulki ta APC da na abokin karawarsa na jam’iyyar adawa ta PDP.

Majiyarmu ta shaida mana cewa rikincin ya barke ne bayan an kashe wani  jigo a jam’iyyar APC a yankin Oba Nla a garin na Akure a ranar Asabar da dare.

Arangamar ta yi sanadiyar jikkata mutane da dama da kuma lalata motoci masu yawa bayan da rikicin ya yadu zuwa yankin Ehrakale.

Hatsaniyar na zuwa ne kasa da mako guda kafin ranar zaben gwamna a jihar ta Ondo, wanda manyan jam’iyyun ke kokarin ganin sun lashe.

Yanzu haka tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da dan takarar Gwamnan jihar a Zaben da ya gabata, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) sun hallara a garin na Akure domin nema wa dan takaran jam’iyyar adawa na PDP goyon baya.