✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta tabbatar da Kawun Davido a kujerar Gwamnan Osun

Kotun ta kori karar da tsohon Gwamna, Oetola da ke kalubalantar cancantar Adeleke na tsayawa takara a zaben.

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a zaben Gwamnan Jihar Osun da aka gudanar a 2022.

Kotun Kolin ta kuma yi watsi da karar da tsohon Gwamna, Adegboega Oetola na Jam’iyyar APC ya shigar na kalubalantar cancantar Adeleke na tsayawa takara a zaben.

Ta kuma caccaki Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Osun da ta ki amfani da hukuncinta na farko kan halaccin taakarar Adeleke.

Adekele kawu ne ga fitaccen mawakin Najeriya, Davido, wanda kuma ya yi a fadi-tashi tun lokacin yakin neman zaben kawun nasa.

Ko a makon jiya mawakin ya addu’ar samun nasara  ga kawun nasa, wanda wasu ke wa lakabi da gwamnan mai rawa.