✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamnan Osun: Dan takarar PDP ya jefa kuri’arsa

Karo na biyu ke nan da Sanata Adeleke ke haduwa da Adeleke a akwatin zabe, duk da cewa a 2018 ya sha kaye

Dan takarar Gwamnan Jihar Osun  na Jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke ya jefa kuri’arsa.

Sanata Adeleke ya kada kuri’a ne da misalin karfe 9 na safe a rumfa ta tara, mazaba ta biyu da ke Karamar Hukumar Abogunde Saga Ede ta Kudu.

Karo na biyu ke nan da Sanata Adeleke ya fito neman kujerar Gwamnan Jihar, kuma suna bugawa da Adegboyega Oyetola, dan takarar jam’iyyar APC kuma gwamna mai ci.

A zaben 2018 INEC ta bayyana Oyetola a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’a 255,505 inda ya kada Adeleke mai kuri’a 255,023 bayan an yi zabe zagaye na biyu a wasu rumfunan zabe bakwai a wasu kananan hukumomi hudu.

An yi zagaye na biyu a lokacin ne bisa zargin magudi da cin zarafin masu zabe.

An yi zagaye na biyu ne bayan da farko a zaben da ba a kammala ba Adeleke na kan gaba da tazarar kuri’a 353 bayan ya samu kuri’a 254,698, Oyetola kuma na da 254,345.

INEC ta ce zaben bai kammala ba ne saboda yawan kuri’u da aka soke ya fi tazarar da ke tsakanin kuri’un ’yan takarar yawa.

Yanzu dai ga shi sun sake haduwa a akwatin zabe, kuma ana ganin Sanata Adeleke na da kishirwan ganin ya kada Mista Oyetola domin huce haushi.