✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Amurka: Yadda Trump da Biden suka ja daga

An yi hasashen Biden na da mafi rinjayen nasara a jihohin mafi muhimmanci a siyasar kasar.

Hankalin duniya ya karkata wajen kirdadon sakamakon zaben Shugabancin Kasar Amurka da ake sa ran bayyanarsa a nan gaba yayin da masana ke ganbin zaben a matsayin raba-gardama kan salon jagoranci da manufofin Amurka da Shugaba Donald Trump ya alakanta da su.

Galibin masu bayyana ra’ayi da kuma yanayin kuri’un da aka kada musamman a jihohi masu tasiri ta fuskar muhimmanci ga makomar sakamakon zaben, sun nuna nasara ga dan takarar jam’iyyar Democrat kuma Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Joe Biden fiye da yadda ake jingina wa dan takarar jam’iyyar Republican, wato Shugaba Trump.

Sakamakon zaben na farko-farko daga sassan jihohin Kentucky da Indiana, ya nuna cewa Trump ne a kan gaba, sai dai hakan ba a bin mamaki ba ne kasancewar jihohin na da fadi da kuma zurfi inda galibin al’ummar yankin sun fi dangwala wa dan takarar jam’iyyar Republican kuri’unsu.

Sakamakon baya-bayan nan na nuna cewa babu wanda ya bayar da tazarar da za ta ba shi damar lashe zaben kai tsaye yayin da a jihohin da ’yan takarar ke bukatar lashewa muddin suna son cin wannan zaben kamar Florida da Michigan da Ohio, babu wanda ya yi wa abokin karawarsa fintinkau.

Da yiwuwar Pennsylvania ta raba gardama

A yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon tun a daren Talata, masu sharhi na kamfanin labarai na Amurka (CNN), sun ce da yiwuwar jihar Pennsylvania za ta raba gardama kasancewarta ita ce Shugaba Trump ke matukar bukata domin samun nasara.

Da a ce Trump ya yi nasara a jihar Florida, Georgia da North Carolina, inda Biden ya ba shi ’yar gajeruwar tazara a jihohi biyu daga uku, dole yana bukatar samun nasara a Arizona da Pennsylvania domin samun adadin kuri’un da za su ba shi damar lashe zaben.

Domin rusa wannan lissafi, Biden a ranar Talata ya ziyarci mahaifarsa ta Pennsylvania domin tabbatar da cewa Trump bai ci shi da yaki ba a gida.

Manufar Biden da jam’iyyar Democrat ita ce samun nasara a jihohin Pennsylvania, Michigan da Wisconsin doriya a kan jihar Illinois wadda ba su da shakku a kanta.

A shekarar 2016, Trump ya lashe zaben a uku daga cikin jihohin da a yanzu Biden ya ke hankoro, kuma hasashe na nuna cewa jam’iyyar Democrats ce za ta yi nasara.

Masu sharhi na CNN sun yi hasashen Biden na da mafi rinjayen nasara a jihohin mafiya muhimmanci a siyasar kasar yayin da ake hasashen Trump zai lashe jihar Florida ganin cewa an kirga fiye da kashi 90 cikin 100 na kuri’un jihar kuma yana kan gaba.

Matukar Biden bai yi nasara ba a jihohin Pennsylvania da Florida, inda  Shugaba Trump zai dage don ganin ya samu nasara a cikinsu, Biden ka iya samun nasara a jihohin Michigan, Wisconsin da Arizona.

Alkalumma sun nuna cewa wadannan jihohi biyar sune mafiya muhimmanci a siyasar kasar gami da North Carolina da Georgia.

Kawo karshen mulkin Trump

Ana ambaton wannan zabe a matsayin wanda zai kawo karshen salon mulki da manufofin Shugaba Donald Trump.

A yayin da galibin masu dangwala wa jam’iyyar Republican kuri’unsu suka hankoron ganin Shugaba Trump ya ci gaba da rike mulkin kasar Amurka, mafi rinjayen kaso na masu goyon bayan jam’iyyar Democrats sun daura damarar ganin Trump ya sauka daga kujerar mulki ba don suna goyon bayan Biden ba.

A halin yanzu dai akwai ra’ayoyi mabanbanta kan zaben Amurka a fadin duniya, inda yadda dangartarkar Trump da ta galibin sassa na duniya ta yi tsami sakamakon rashin jituwa a kan yarjejeniya ta akida da manufofin jagoranci.

Daga bangaren Yammacin Turai, kawayen Amurka na son kawo karshen mulkin Shugaba Trump a yayin da dangartaka ta yi tsami musamman da kungiyar kawancen tsaro ta NATO da sauran masu kawanceceniya da Amurka.

Haka kuma Amurka ta zame hannunta daga yarjejeniyar sauyin yanayi, wanda hakan ya kara tsamin dangartaka tsakanin Amurka da kawayenta.

A bangaren Gabashin Turai, yadda Trump ya jajirce don ganin ya faranta wa Shugaban Rasha, Vladmir Putin, ya fusata da yawa daga cikin kasashen yankin.

Alkawalin da Trump ya yi a lokacin yakin neman zabensa a 2016, na gina ganuwa a tsakanin Amurka da Mexico, ya fusata makociyar kasar da kuma Amurkawan Latin baki daya.

A Gabas ta Tsakiya, Isra’ilawa na goyon bayan Trump wanda ya dauke Ofishin Jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus, wanda kudirin hakan ya samar da zaman lafiya a yarjejeniyar sulhu a Gabas ta Tsakiya da karfafa gwiwar Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain, da Sudan domin gyara dangartarkarsu da Isra’ila.

Ya kuma zare Amurka daga yarjejeniyar Makaman Nukiliyar Kasar Iran, duk da ci gaba da goyon bayan manyan kasashen Turai.

A bangare guda kuma, haramcin shiga Amurka da Trump ya yi wa musulmi bakin haure daga kasashe da dama da ke da rinjayen Musulmi, ya kara nisanta shi da Musulmi a duniya.

Trump ya kuma kaurace wa taron Asiya da Pacific, inda ya dauki dogon lokaci yana yaki a kan kasuwanci da kasar China yayin da kuma ya yi watsi da kasashen nahiyyar Afrika kusan gaba daya.