✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Amurka: Yadda muhawarar Trump da Biden ta buge da zage-zage

Muhawara tsakanin Donald Trump da Joe Biden ta kare da zarge-zarge da ma zage-zage

Mahawarar farko ta ’yan takarar shugabancin kasar Amurka a tsakanin Donald Trump na jam’iyyar Republican da Joe Biden na jam’iyyar Democrat ta kare da zage-zage da tonon silili.

Biden ya kira Trump “wawa” da “makaryaci” a daidai lokacin da shi kuma Trump mai neman tazarce ya jefe shi da cewar an sallami dansa daga aikin soja saboda shan kwaya.

“Duk abin da yake fada mana karya ce. Ban zo nan don in saurari karyarsa ba,” inji Biden.

Wani babban dan jarida mai aiki da gidan talabijin na Fox, Chris Wallace, ne ya ja akalar muhawarar wadda aka kwashe minti 90 ana tafkawa, kuma ta tabo wasu muhimman abubuwan da ’yan kasar suka dade suna neman amsarsu.

Ana zaton wuta a makera

Galibin mutane sun tsammaci zafafan kalaman da Biden ya furta za su fito daga bakin Shugaba Trump ne, saboda yadda kurarsa ta koka a kan hakan.

Sai dai Trump ya kasa yin shiru a lokacin da Biden ya ce, “Ka yi wa mutane shiru”, ya kuma kara da cewa “kai ne shugaban kasa mafi lalaci da Amurka ta taba yi”.

Cikin hassala Trump ya mayar da martanin cewa, “Kai gabo ne kuma mafi koma baya a ajin da ka kammala karatunka, saboda haka kada ka kara jifan wani da kalmar rashin basira”.

Badakalar haraji

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa Shugaba Donald Trump bai biya haraji ga gwamnatin tarayya ba na shekarun 2016 da 2017.

Mai jagorantar muhawarar ya bukaci Trump ya bayar da amsa kai-tsaye a kan cewa shin ya biya harajin da kimarsa ta zarce Dala 750?

Da fari Trump ya nemi ya zame amma da ya ga ba makawa dai ya ce, “Na biya miliyoyin Daloli”.

Wuf, sai Biden ya ce, “Ka nuna mana shaidar da ka karba ta biyan harajin”.

Biden ya fitar da shaidar biyan harajinsa da na matarsa da suka biya a shekarar 2019, wanda kimarsa ta kai Dala 300,000.

“Za ka gan shi”, inji Trump.

Amma bai fadi ranar da zai gabatar da shi ba.

Wannan muhawara ce dai ta farko a cikin uku da aka shirya wa ’yan takarar kafin a gudanar da zaben na 2020.

Ra’ayoyin jama’ar kasa sun yi nuni da cewa Biden ya yi nasara a muhawarar da kashi 48 cikin 100 inda ya doke abokin hamayyarsa Shugaba Trump mai kashi 41, sai kuma sauran ’yan takara biyu da suka yi kankankan da kashi 10 cikin 100.

Karin tambayoyi

Da farko Wallace ya tambayi Shugaba Trump ko yana da hurumin nada makwafin marigayiya Mai Shari’a Ruth Bader Ginsburg a Kotun Kolin Amurka.

Mista Trump ya ce cin zaben shugaban kasa yana da matukar tasiri, “Mu muka lashe zaben, saboda haka muke da damar nada Alkalin Kotun Kolin”.

A nashi ra’ayin, Biden ya bukaci a jinkirta maganar zabar alkalin har sai an kammala zaben shugaban kasa, don duk wanda ya yi nasara ya nada shi.

Ya kuma ce ta wannan hanyar ce kadai Amurkawa za su samu bayyana ra’ayoyinsu na zabar wanda su ke son ya yi shugabancin kasar da mataimakinsa.

Wallace ya hassala Trump

Trump ya hassala da tambayar da mai jan akalar muhawarar ya yi masa cewa bai yi maganar tsarin kiwon lafiya ba.

Idan ba a manta ba, Shugaba Trump ya dade yana yi wa Amurkawa romon baka cewa zai samar da tsarin tun farkon hawansa mulki.

Da budar bakinsa, sai Trump ya ce, “Na yi mana. Lallai na yi.”

Shi kuwa Wallace sai ya ce, a matsayinsa na mai jan akalar shirin, “Ina bukatar ka da ka amsa tambayar da na yi maka”.

Tambayar da kuma sukar wata dokar da Shugaba Trump ya sanya wa hannu kwanan ta hassala Trump, inda ba tare da bayar da wata gamsasshiyar amsa ba, ya ce, “Bisa dukkan alamu, da kai za mu yi wannan muhawarar ba ni da Joe Biden ba.”

Wannan martini na Shugaba Trump ya tunzura Biden, wanda ya ce “Rufe mana baki malam”.

Tambaya a kan Covid-19

A lokacin da ’yan takarar suke amsa tambaya a kan tsarin da za su aiwatar a shekara mai zuwa don kawo karshen annobar COVID-19 a Amurka, Biden ya ce, “Shugaban kasar nan ba shi da tsayayyen shirin tunkarar matsalar”.

Daga farkon annobar COVID-19 kawo yanzu, Amurkawa fiye da 200,000 cikin miliyan bakwai da suka kamu suka rasa rayukansu.

Mutanen da suka halarci muhawarar

Bisa la’akari da annobar COVID-19, mutane kadan ne suka halarci muhawarar, tare da makusantan ’yan takarar, ciki har da iyalansu.

Matar shugaba Trump, Melanie, da matar Joe Biden, Jill, sun halarta.

Haka nan kuma an bi sharuddan kariya daga annobar wanda a dalilin haka ko hannu ’yan takarar ba su yi ba kamar yadda aka saba.