✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Abuja: Dan jaridar da ke daukar hoton masu sayen kuri’a ya sha da kyar

Sun dai yi barazanar dukansa, muddin bai dena daukarsu ba.

Yayin da ake ci gaba da gudanar da zaben Kananan Hukumomi a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja, wasu matasa da ake kyautata zaton ’yan dabar siyasa ne sun yi barazanar lakada wa dan jaridar da ke aiki da jaridar Daily Trust dukan tsiya.

Lamarin dai ya faru ne da dan jaridar mai suna Idowu Isamotu ranar Asabar a makarantar firamare ta LEA da ke Ikwa a yankin Zuba da ke Gwagwalada.

’Yan dabar dai sun yi barazanar dukansa ne saboda yadda suka ce yana kokarin daukar su a hoto, a daidai lokacin da jam’iyyar da suke goyon baya take tsaka da raba wa mata kudade domin su zabe ta.

Dan jaridar dai na daga cikin wadanda Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta tantance domin su dauko rahoton zaben, kuma ya je rumfar zaben ne da nufin ganin me ke wakana a can.

Dan jaridar dai ya ce mutanen na ta kokarin raba kudaden ne a filin Allah Ta’ala.

An dai jiyo daya daga cikin ’yan dabar na cewa, “Kana kokarin daukar abin da ke faruwa ko? Muddin baka bari ba, za mu tabbatar ka bar nan wajen da raunuka a jikinka.”

Hakan ne yasa Idowu ya gaggauta barin wajen tare da sanar wa jami’an tsaro abin da ke faruwa.