✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu shiga yajin aikin har sai abinda hali ya yi ranar Juma’a — Ma’aikatan Jami’a

Yajin aikin na sai baba ta gani zai fara ne daga karfe 12 na daren ranar Juma’a.

Gamayyar Kungiyoyin Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya sun kammala washin wukarsu ta shiga yajin aikin sai baba ta gani a ranar Juma’a, 5 ga watan Fabrairun 2021.

Kungiyoyin da suka hada da na manyan ma’aikata SSANU da kuma ma’aikata marasa koyarwa a jami’oin kasar NASU sun yanke hukuncin haka ne sakamakon watsi da bukatunsu da gwamnatin tarayya ta yi.

A yayin zantawarsa da Aminiya ta hanyar wayar tarho, Shugaban SSANU Muhammad Haruna Ibrahim, ya ce sun yanke shawarar tsunduma yajin aikin a yayin wani taro na cimma matsaya da suka gudanar a tsakanin shugabancin kungiyoyin biyu a ranar Alhamis.

Mista Haruna ya ce an aike da wasikar umartar dukkanin ’ya’yan kungiyoyin da su bayar da hadin kai domin tabbatar da an gurgunta harkokin ilimi a jami’o’in kasar daga ranar Juma’a.

Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ta gaza tabbatar da jarjejeniyar da suka kulla bayan wa’adin kwanaki 14 da suka bata domin ta waiwayi bukatunsu.

Shugaban na SSANU ya ce yajin aikin na sai baba ta gani zai fara ne daga karfe 12 na daren ranar Juma’a madamar ba a samu sauyin kudiri ba a tsakanin rassanta da ke fadin kasar.

Idan ba a manta ba a watan jiya na Janairu ne gamayyar kungiyoyin ma’aikatan suka gudanar zanga-zangar lumana domin yi wa gwamnatin tarayya matsin lambar warware bukatunsu da suka hada tsarin raba Naira biliyan 40 na alawus-alwawus a tsakanin ’ya’yanta da na kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.

Sauran bukatun da matsalolin da kungiyoyin ke bukatar ganin an shawo kansu sun hada da takaddamar da ta dabaibaye sabon Tsarin Biyan Albashi na bai daya (IPPIS), inda da dama ake zaftare wani kaso na albashinsu da ake biya ta wannan tsari.