✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kama duk wanda ya dauki makami ranar zabe a Kano —’Yan sanda

Ya bayyana hakan ne a Jihar Kano, a ci gaba da shirye-shirye da rundunar ke yi na tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da…

Mataimakin babban sufeto-Janar na ’yan sanda DIG Hafiz Muhammad Inuwa da ke kula da harkokin zaben shekarar 2023 a yankin jahohin Arewa maso Yammacin Najeriya, ya gargadi ’yan siyasa da magoya bayansu, da su kauce wa yin wani abu da zai tada hankulan masu zabe. 

DIG Hafiz M. Inuwa ya bayyana cewa shugaban ’yan sanda Usman Alkali Baba ya umarce su, da su gargadi ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki da su ja wa magoya bayansu kunne gabanin zaben da ke tafe a ranar Asabar 18 ga watan Maris 2023.

Ya bayyana hakan ne a Jihar Kano, a ci gaba da shirye-shirye da rundunar ke yi na tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu.

Ya kara da cewa fatansu, shi ne a yi zabe lafiya a kammala lafiya, ba tare da nuna siyasa da gaba ba.

“Duk wani dan siyasa in dai yana son ci gaban Kano, to zaman lafiya shi ne ci gaban, so ake a zauna lafiya.

“Kuma na zo da jawabi, in gargade su, Wallahi ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen maganin duk wani da ya nemi ya tada fitina,

“Saboda haka ina tabbatar muku da cewa duk wanda ya nemi ya dau makami ko don ya hana wani fitowa zabe, ko don ya jikkata wani, to Wallahi Tallahi fushin hukuma ne a tattare da shi” in ji shi.

Ya ce ba zu raga wa kowa ba duk girmansa kowaye , domin ci gaban Nijeriya da ci gaban Kano da kuma zaman lafiya shi ne agaban mu.

“In kunne ya ji jiki ya tsira, wanda kuma yake ganin zai yi wani abu akasin haka to ga fili ga mai doki,” in ji DIG Hafiz M. Inuwa.

Tun kafin wannan lokacin ne Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa sun tanadi ’yan sanda masu yawa don tabbatar da tsaro a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.