✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kafa cibiyar horar da ma’aikata —Abba Gida-Gida

An tafka ta’asa da nuna son kai a fagen daukar ma’aikata a gwamnatin Ganduje.

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa za ta himmatu wajen gyara ma’aikatun gwamnati a wani yunkuri na karfafa tsarin samar da ayyuka masu inganci.

Abba Kabir wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya bayyana cewa, “kamar yadda yake a cikin tsarinmu, za mu kafa Cibiyar Horar da Ma’aikatan Gwamnati don dacewa da mafi kyawun ayyuka na duniya.”

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaran Zababben Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu.

Zababben Gwamnan ya taya ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da ke jihar murnar zagayowar Ranar Ma’aikata ta shekarar 2023.

Ya ce ma’aikata su ne jigon samar da shugabanci nagari a duk wani tsarin dimokuradiyya, don haka sun cancanci a yaba musu bisa sadaukarwar da suke yi wajen gudanar da aikinsu.

Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba wa ma’aikatan jihar tabbacin samun ingantacciyar walwala da ya hada da gaggauta biyan albashi da fansho daga gwamnatin Jam’iyyar NNPP mai jiran gado.

Injiniya Abba ya ce gwamnati mai jiran gado na sane da matsalolin da ma’aikatan jihar ke fuskanta da suka hada da rashin kyawun yanayin aiki da rashin isassun ma’aikata da dai sauran matsaloli wanda kuma ya yi alkawarin gyara su.

Zababben Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta sake duba duk wasu ayyukan da ba su dace ba tare da tabbatar da samar da sahihin tsarin daukar ma’aikata ga duk ’yan Jihar Kano da suka cancantar shiga aikin gwamnati.

“Dangane da yadda ake tafka ta’asa da nuna son kai a fagen daukar ma’aikata da gwamnatin mai barin gado ke aikatawa, wannan ma bangare ne da yake bukatar kulawarmu.”

Zababben Gwamnan ya ajiye aikin gwamnati sama da shekaru 10 da suka gabata, bayan ya shafe sama da shekaru 20 yana aiki a wurare daban-daban musamman a Ma’aikatar Ruwa ta Jihar Kano .