✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu hukunta DCP Abba Kyari —Shugaban ’yan sanda

Shugaban ’yan sandan ya ce ba sani ba sabo wajen daukar mataki.

Hukumar ’Yan Sandan Najeriya ta ce za ta dauki matakin da ya dace kan jami’inta, DCP Abba Kyari da ta tadakar, muddin ta same shi da laifin da ake zargin sa da aikatawa.

Hukumar ta yi wannan bayani ne bayan karbar wani rahoto na musamman da kwamitin da ta kafa kan binciken DCP Abba Kyari ya gabatar mata.

Babban Sufeton ’Yan Sandan ne ya karbi rahoton kan DCP Abba Kyari wanda aka dakatar bayan an zarge shi da karba rashawa a wajen Hushpuppi, wanda ake zargi da damfara a kasashe.

Rundunar ta kafa wani sabon kwamiti da zai yi nashi binciken kan zargin da Amurka ta yi wa Abba Kyarin wanda ya musanta.

A ranar Alhamis ne Mataimakin Shugaban ’Yan Sanda, Joseph Egbunike ya mika rahoton sai dai ba a bayyana me rahoton ya kunsa ba.

Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali ya yi alkawarin hukunta Abba Kyari, matukar aka same shi da laifi.