✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

 Za mu gurfana a kotu da wanda ya yi min kazafi —Kamaye

Ba na son Dattawan Kannywood su sa baki a wannan lamari.

Dan Azumi Baba wanda aka fi sani da Kamaye a cikin shirin nan mai dogon zango na Dadin Kowa, yana shirin garzayawa Kotu don kai karar wanda ya bayar da labarin cewa ba shi da lafiya.

A bayan nan ne dai wani labari ya bayyana cewa rashin lafiyar ta sa mawaki Hamisu Breaker ya ba shi miliyan biyar, sannan kuma jarumi Ahmed Lawan ya ba shi Naira dubu dari biyu don ya nemi magani.

A hirarsa da Aminiya, Dan Azumi Baba ya ce zai dauki matakin ne don kotu ta bi masa hakkinsa kan wannan kazafi da ka yada a kansa.

Ya ce  “Wannan ba shi ne karon farko ba da wannan mai labaran karya ya ce ba ni da lafiya ba, kuma an bani wasu kudade don neman magani.

“A baya, cewa ya yi gwamnatin Jihar Kano ta yi min alkawarin miliyan biyar in nemi magani, sannan kuma ya sa hotona da na gwamnan Kano da kuma na Baba Impossible a bidiyon. Sai kuma yanzu ga wannnan sabon kazafin.”

Tuni Dan Azumi Baba ya aika da wani sako na wannan aniya ta sa ga Kungiyar Dattawan ‘yan fim tare da nemansu da kar su sa baki domin ba zai hakura ba.

A cewarsa, ya aika sakon aniyarsa tasa ce ga Kungiyar Dattawan don ko a nan gaba mai wannan batancin zai nemi da su sa baki ya janye ganin cewa ya dauki mataki na shari’a.

Kamaye ya ce tuni sun gama magana da lauyansa kuma nan ba da dadewa ba za su gurfana a gaban da alkali da mai wannan Kazafi.

Kazalika, ya yi haka ne don ya yi wa tufkar hanci saboda gaba.