✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ba ’yan kabilar Igbo kariya a Kano —Sarkin Bichi

Sarkin na Bichi ya bayyana farin ciki da godiyarsa ga masu rike da sarautun gargajiya na Jihar Inugu.

Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, ya yaba da yadda Gwamnan Jihar Inugu, Ifeanyi Ugwuanyi ya nuna gamsuwa da yadda al’umar Igbo ke amfana da tsarin zaman lafiya a Arewacin Najeriya tun lokacin zuwan gwamnatinsa. 

Sarkin ya yaba wa Gwamna Ugwuanyi da cewa gwamnatinsa ta himmatu wurin hada kai da kuma wanzar da zaman lafiya tsakanin ‘yan Najeriya ba tare da la’akai da bambancin addini, kabila ko siyasa ba.

Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kara da cewa, “Mutanen yankin Arewa har abada ba za su taba mantawa da irin salon nagartaccen mulkinsa ba”.

Sarkin ya yaba tare da godiya ga sarakunan gargajiyan jihar Inugu da cewa “Bayanan da muke samu game da al’umarmu mazauna yankin mai dadi ne; muna godiya kwarai da gaske”.

Sarkin ya yi wannan jawabin ne yayin da Gwamna Ugwuanyi ya karbi bakuncinsa a fadar gwamnatin Jihar Inugu.

Ya jaddada wa Gwamna Ugwuanyi, cewa “Ka zo Jihar Kano, za mu kare maka muradinka, mu tabbatar maka cewa al’umar Igbo da sauran kabilun Najeriya suna zaune cikin aminci a Jihar Kano”.

A nasa jawabin, Sarkin Inugu, ya ce ziyarar Sarkin Bichi za ta karfafa dangantar mahaifin Sarkin Bichi, Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero da al’umar Igbo musanman lokacin da yake Uban Jami’ar Nsukka (UNN) sama da shekaru 20 a lokacin rayuwarsa.

“Ziyarar Sarkin Bichi za ta cike wani gibi da ke tsakanin al’umar Arewacin Najeriya da Gabashin kasar.

“Za mu ci gaba da ririta wannan alakar da cike gibin don tabbatar da zaman Najeriya a matsayin kasa daya duk da bambance-bambancen da ke tsakaninmu, za kuma mu ci gaba da zama a matsayin abokan juna cikin yardar Allah”.