✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a kayyade farashin wutar lantarki da iskar gas a Birtaniya

Za a kayyade farashin kowane megawatt na lantarki a kan Fam 211, iskar gas kuma Fam 75.

Gwamnatin Birtaniya ta ce daga watan Oktoban 2022, za ta daidaita farashin wutar lantarki da iskar gas ga ’yan kasuwa, sakamakon tashin gauron zabo da makamshin ya yi a kasar.

Ministan kudin Birtaniya, Kwasi Kwarteng ya bayyana a ranar Laraba cewa za a kayyade farashin kowanne megawatt na lantarki a kan Fam 211, iskar gas kuma Fam 75.

“Mun yi haka ne domin tallafa wa kamfanonin da suka kusa durkushewa da kuma takaita hauhawar farashin kayyaki a Birtaniya.

“Gwamnati za ta biya tallafi ga masu samar da makamashin da suka rage farashin ga abokan huldarsu da ba na cikin gida ba,” in ji ministan.

Shirin dai zai fara aiki ne daga ranar 1 ga Oktoba, 2022 zuwa 31 ga Maris 2023, ga duk masu amfani da makamashin daga kungiyoyin agaji da makarantu da asibitoci da kasuwanni.