✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara daurin rai-da-rai ga masu fasakwaurin ababen fashewa Najeriya

Sabuwar dokar ta tanadi hukuncin daurin rai-da-rai ba tare da zabin biyan tara ba

Majalisar Dattawa ta amince da kudurin dokar yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga masu fasakwarin ababen fashewa zuwa Najeriya.

Kudurin ya samu amincewa ne bayan majalisar ta karbi rahoton da kwamitin da Sanata Tanko Al-Makura ya jagoranta kan gyaran fuska ga dokar gudanarwa, sarrafawa, amfani, kasuwanci da kuma mallakar ababen fashewa ta shekarar 1964.

Sabuwar dokar ta tanadi “hukuncin daurin rai-da-rai ba tare da zabin biyan tara ba, ga duk wanda ya aka samu da laifin kera abun fashewa ba bisa ka’ida ba.”

A yayin gabatar da rahoton a madadin shugaban kwamitin, Sanata Adelere Oriolowo, ya alakanta yaduwar manyan laifufa a Najeriya da matsalar fasakwauri da fataucin haramtattun abubuwan fashewa.

Ya bayyana cewa an kai matakin da ’yan ta’dda da sauran masu laifi suke amfani da sabbin dabaru da kuma abubuwan fashewa wajen aikata ta’asarsa.

A dalilin haka, ya ce, ’yan Najeriya da dama sun rasa rayukansu a sassan kasar a lokuta daban-daban.