✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a daure ‘barayin’ kayan NYSC shekara uku

Shugaban Hukumar Masu Yi wa Kasa Hidima (NYSC), Birigediya Shu’aibu Ibrahim ya ce duk wanda aka kama da kayan hukumar to za a yanke masa…

Shugaban Hukumar Masu Yi wa Kasa Hidima (NYSC), Birigediya Shu’aibu Ibrahim ya ce duk wanda aka kama da kayan hukumar to za a yanke masa hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari.

Ya bayyana haka ne bayan wasu zauna-gari-banza sun haura sananin NYSC da ke Kubwa a Abuja, da sunan neman kayan tallafi, suka wasashe abubuwa daga dakin ajiyar sansanin.

“Ba mu da kayan tallafin COVID-19 a sansaninmu.

“Abun takaici sun sace kayan da ake amfani da su domin ba da horo.

“Doka ce duk wanda aka kama da kayan masu yi wa kasa hidima [ba bisa ka’ida ba] zai fuskanci hukuncin shekara uku a gidan yari”, cewarsa.

Ya kara jan hankalin bata-garin da suka kwashi kayayyaki a sansanin da cewa lallai su dawo da su kafin bincike ya gudana.

Ya ce an kafa hukumar ce domin yi wa kasa hidima da samar da ci gaban kasa, don haka ba su da wata alaka da kayan tallafin annobar COVID-19.