Ana rajistar masu zabe a halin yanzu mene ne makasudin yin haka?
Wato wannan shiri na bai wa ’yan kasa katin zabe an fara shi ne tun a watan Afrilun bara. Shiri ne da Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta kaddamar da shi domin bai wa ’yan kasa da ba su samu damar yin rajistar zabe ba a lokutan baya sakamakon wani dalili kamar na rashin cika shekara 18 a lokacin damar su yi rajistar a yanzu. Na biyu kuma sai wadanda suka yi rajstar amma sai katin ya lalace a dalilin wata tawaya ko ya salwanta, su ma su zo su gabatar da koke-kokensu saboda hukuma ta sake ba su wani a madadin na baya. Na uku kuma wannan shiri ne da zai bai wa ’yan kasa da suka yi rajista a baya amma sai suka sauya matsugunni wato mahallinsu a yanzu, ya alla daga wani gari ne zuwa wani gari ko kuma unguwa ko ma jiha baki daya, sannan suke da burin idan Allah Ya kai mu shekara ta 2019 za su yi zabensu a sabon wurin da suka sauya. Wadannan su ne dalilan yin rajisatar a wannan karo.
Zuwa wane lokaci ne shirin rajistar zai kawo karshe?
Kamar yadda na yi bayani a baya an fara wannan aiki ne tun a ranar 23 ga watan Afrilun bara , kuma za a ci gaba da yin sa har zuwa kusa da ranakun fara zabe na badi (2019). Ga dokar zabe, hukumar na da damar ci gaba da aiwatar da shirin har zuwa ranaku 60 kafin zabe. Sai a nan gaba ne Hukumar INEC za ta sanar da ranar da za ta dakatar da rajistar.
Kamar a wadanne wurare ne ake yin rajistar?
Da farko an fara aikin ne a hedikwatocin hukumar zabe da ke kananan hukumomin kasar nan 774, amma daga baya sakamakon korafin da jama’a suka rika yi cewa wuraren sun gaza, hukumar ta kara adadin da wasu wurare 602 bayan ba da damar yin hakan ga ofisoshin hukumar a jihohi wadanda su ne ke da alhakin zabar wuraren da suka ga sun fi da cewar su kara, inda kuma ake gudanar da wadannan ayyuka a yanzu.
Wane lokaci ne aka yi karin?
An yi karin ne a lokuta biyu duk a ckin shekarar da ta gabata. Da farko an yi karin ne a wurare 302 sai kuma daga bisani aka kara a wurare 307.
Akwai korafin cewa masu yin rajistar na sauya matsuguni alhali mutane da dama ba su samu damar yin rajistar ba?
Abin da ya faru shi ne; bayan la’akari da yadda fadin kasar yake, sai aka bai wa jami’an a matakin yankuna damar sauya wurin rajista idan suka kula cewa sun gamsar da mutanen yankin da suka fara don kai wa ga wasu al’ummar da aka kula ba su samu damar yi ba. Kuma an ba da hurumin sauya wurin ne ga ofishoshin yankuna da ba sai mu a mataki na kasa mun sa baki ba. Sai dai za mu yi amfani da wannan dama wajen fadakar da jama’a cewa ba sai sun kuntata wa kansu ba wajen turereniya a yayin wannan aikin, ya kamata su ni wannan aikin za a ci gaba da yin sa har zuwa daf da lokacin zabe na gaba.