✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunwa na ci gaba da ta’adi a Somaliya —MDD

Farin da ake fuskanta a kasar Somaliya ya kasance mafi muni a tsawon shekaru 50 da suka gabata.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yunwa tana ci gaba da ta’adi sakamakon farin da ake fuskanta a kasar Somaliya.

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce farin da ake fuskanta a Somaliya ya kasance mafi muni ga kasar cikin shekaru 50 da suka gabata.

A wannan Talata mai magana da yawun asusun, James Elder ya ce ana bukatar kimanin kudi Dalar Amurka miliyan dubu biyu saboda a tunkari matsalar.

Jami’in asusun na UNICEF ya kara da cewa a watan Agustan da ya gabata kadai kimanin yara 44,000 aka kwantar a asibiti sakamakon matsananciyar yunwa.

Kimanin mutane miliyan takwas, kusan rabin mutanen kasar ta Somaliya farin ya shafa a cewar Majalisar Dinkin Duniya, dama kasar tana cikin tashe-tashen hankula na tsageru masu kaifin kishin addinin Islama.