✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yunkurin tsige Buhari babban abin takaici ne – Shugaban APC

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana yunkurin da wasu ‘yan majalisa ke yi na tsige Shugaban Kasa Muhammadu Buhari…

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana yunkurin da wasu ‘yan majalisa ke yi na tsige Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin abin takaici. 

Shugaban Jam’iyyar ya yi wannan furuci ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust TV a Abuja a ranar Talata.

Abdullahi Adamu, wanda tsohon dan Majalisar Dattijai ne, ya ci gaba da cewa wannan yunkuri da ‘yan majalisar ke kokarin yi a bisa furucinsu, abin Allah-wadai ne, kuma sun sauka daga kan tsarin da ya dace.

“Tsige shugaba kan karagar mulki ba birgewa ba ne, illa takaici, [kuma] an daina yayinsa.

“Kodayake da irin wannan majalisar ta kasa, babu mamaki idan sun yi [wannan yukuri]. Hakan na faruwa ne a kowanne mulki na dimukuradiya, amma wadanda suka soma, tuni suka daina,” inji Shugaban na APC.

A kwanan baya ne wasu ‘yan Majalisar Dattawa daga jam’iyyar PDP suka yi barazanar tsige Shugaba Buhari idan ya gaza magance matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya a cikin wa’adin makwanni shida.

‘Yan Majalisar sun yi wannan ikirari ne a wani taron ‘yan jarida kafin majalisar ta tafi hutun wata biyu.