✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kishi ya sa wata mata cinna wa kanta wuta a Jigawa

Ta yi wanka da fetur ta cinna wa kanta wuta saboda mijinta zai dawo da tsohuwar matarsa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce an kwantar da wata mata a asibiti bayan da ta yi yunkurin kashe kanta a Karamar Hukumar Dutse ta Jihar.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Dutse.

  1. Yajin aikin likitoci ‘shirme’ ne —Ngige
  2. Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar Janar Oneya

“A ranar Juma’a, da misalin karfe 10:00 na dare, ’yan sanda sun samu labarin cewa wata mata a kauyen Rungumau, Karamar Hukumar Dutse, ta yi yunkurin kashe kanta, inda ta yi wanka da man fetur sannan ta cinna wa kanta wuta.

“Daga baya kuma ta rika ihun neman a kawo mata agaji inda aka dauke ta zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Dutse (FUD), domin a yi mata magani.”

Shiisu ya ce matar ta yi aika-aikan ne ranar 6 ga watan Agusta, 2021, bayan ta gano cewa mijinta na shirin sake auren tsohuwar matarsa.

Ya kara da cewa, ’yan sanda, bayan samun wannan bayanin, sun je wurin da lamarin ya faru, inda suka garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwar domin kula da ita.

A cewarsa, za a gurfanar da matar a kotu da zarar an sallame ta daga asibiti.