✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yawan shan kwayar Farasitamol na shafar hanta’

Kwamishinan Lafiya na Jihar Binuwai, Dokta Joseph Ngbea ya shawarci yan Najeriya da su kiyayi shan kwayar Farsitamol ba tare da umarnin likita ba. Kwamishinan…

Kwamishinan Lafiya na Jihar Binuwai, Dokta Joseph Ngbea ya shawarci yan Najeriya da su kiyayi shan kwayar Farsitamol ba tare da umarnin likita ba.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne ranar Litinin a taron yaki da shan kwayoyi ba bisa ka’ida ba, wanda cibiyar Eunice Spring of Life (ESLF) ta shirya, tare da hadin guiwar Hukumar yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, a Makurdi babban birnin jihar.

Ya kuma ce hakan ba karamin illa yake wa jiki ba. musamman ma hanta, don haka ya ja hankali kan amfani da kwayoyi da izinin likita kadai, domin gudun illata wani sashe na jiki.

Ya kuma ce ma’aikatar za ta hada guiwa da Hukumar ta NDLEA da kungiyar ESLF, domin mikawa gwamnatin bukatarsu ta gina cibiyoyin gyara hali ga masu shan miyagun kwayoyin a rubuce, a duka mazabun Majalisar Dattijai guda ukun da ke jihar.

A nasa bangaren Gwamnan Jihar, Samuel Ortom, ya alakanta ta`azzarar matsalar tsaro a kasar nan da shan miyagun kwayoyi, in da ya ce ya zamo dole a mike tsaye domin fatattakar sa a kasar.

Jami’ar Kula da Shirye-Shiryen kungiyar ta ELSF, Karen Yankyaa, ta ce wani bincike da aka gudanar a shekarar 2020, ya nuna ’yan Najeriya miliyan 14.4 ke ta’ammali da kwayoyi, da kuma shan su ba bisa ka’ida ba.