✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau saura kwana 47 cif a daina karbar tsoffin kudade

Za a ci gaba da karbar kudin har nan da 31 ga watan Disamba, 2023

A yau Alhamis, 15 ga watan Disamba ce Babban Bankin Najeriya (CBN) zai fara fitar da sabbin kudaden Naira da ya sauya wa fasali, inda mutane za su fara mu’amala da kudin ka’in da na’in.

A ranar 26 ga watan Nuwamban da ya gabata ce dai babban bankin ya sanar da sauya fasalin takardun N1,000 da N500 da kuma N200.

A wancan lokacin dai, bankin ya ce daga ranar ta 15 ga watan Disamba sabbin kudaden za su fara shiga hannun jama’a, kuma za a ci gaba da amfanib da su tare tsofaffin har nan da ranar 31 ga watan Janairun 2023.

Hakan na nufin tsakanin wannan lokacin, duk tsoffin kudaden da suka shiga banki ba za su sake fitowa ba, sannan daga ranar da wa’adin ya cika, za a daina karbar su.

Daga lokacin zuwa makon da ya gabata, CBN ya ce sama da Naira tiriliyan daya a bankunan da mutane suka kai ajiya, kari a kan adadin da suka saba kai wa a baya. Hakan dama na daya daga cikin hanyoyin da bankin ke kokarin bullo da su da nufin takaita zirga-zirgar tsabar kudade a hannun jama’a.

’Yan Najeriya da dama dai sun yi ta bayyana mabanbantan ra’ayoyinsu kan yunkurin bankin, saboda fargabar da suke yi cewa wa’adin da aka diba ya yi kadan, musamman la’akari da cewa ba a ko ina ne ake da bankuna ba a kasar, musamman ma a yankunan karkara, kodayake CBN din ya ce babu gudu babu ja da baya a kan batun.

Bankin dai ya ce daga cikin alfanun da tattalin arzikin Najeriya zai samu, akwai yadda gwamnati za ta san ainihin yawan kudaden da ke yawo a hannun al’umma, ta rage yawan ta’ammali da tsabar kudi, ta rage yawan boye kudi a gida, sannan ta magance yawon kudaden da suka mutu a hannun jama’a.

CBN ya kuma ce sake fasalin kudin zai rage yawan kudaden jabun da suka yawo a hannun jama’a, sannan kuma za su taimaka wajen yai da ta’addanci, kasancewar hatta masu garkuwa da mutane tsabar kudaden suka karba, yanzu kuma dole su kai su banki.

Bugu da kari, wasu ’yan siyasa na fargabar cewa an kirkiro da shirin ne da gangan don a musguna wa ’yan adawa, amma bankin ya ce sam babu kamshin gaskiya a zargin.