✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau NAFDAC za ta fara bincikar Indomie kan ‘hadarin cutar kansa’

NAFDAC za ta fara bincike na ba-zata a kan Indomie bisa zargin taliyar na dauke da sinadarin da ke kawo cutar kansa

A yau Talata Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) za ta fara bincike kan taliyar yara ta Indomie, wanda ake zargi na dauke da sinadarin Ethylene Oxide, mai haddasa cutar kansa.

Shugabar NAFDAC, Farfasa Mojisola Adeyeye, ta ce hukumar za ta fara bincike na ba-zata a masana’antun sarrafa Indomie kan nau’ikan taliyar da kayan hadinsu domin tabbatar da gaskiya.

Hakan na zuwa ne bayan a ranar Litinin, NAFDAC ta sanar da haramta shigo da taliyar Najeriya daga kasashen waje.

Farfesa Adeyeye ta ce hukumarta ta dauki matakin gwajin ne bayan da hukumomin kasar Taiwan da Malaysia suka gano sinadarin Ethylene Oxide, a cikin taliyar a kasashensu.

Ethylene oxide na daga cikin sinadaran da ake amfani da su wajen adana abinci; sai dai kuma yana da barazanar haddasa cutar kansa ga dan Adam.

Shugabar NAFDAC din ta bayyana cewa tuni dakin gwaje-gwajen hukumarta ya fara shirye-shirye domin fara bincike kan sinadarin da aka gano cikin taliyar.

Ta jaddada cewa idan aka kammala binciken, Hukumar za ta bayyana wa ’yan Najeriya abin da ta gano.

Adeyeye ta bayyana cewa, dama gwamnatin Najeriya ta jima da haramta shigo da Indomie daga kasar waje.

“Yanzu kawai kokarin hana fasakwarinsa zuwa cikin kasar nan ake yi, sannan muna gudanar da bincike domin tabbatar da cewa kayan hadin Indomie da sauran nau’ikan taliyar yara da ake sarrafawa a Najeriya ba su da hadari.”

Indomie ba shi da hadari —Kamfani

Sai dai a da yake kare kayan da yake, kamfanin Indofood mai sarrafa taliyar Indomie a Najeriya, ya ce, duk nau’ikan taliyar yara da kamfanin ICBP na kasar Indonesiya na bin ka’idodin sarrafa su da hukumomin kula abinci na kasar da suka shimfida.

Sanarwar Indofood ta ce, “ICBP ya fi shekara 30 yana fitar da taliyar yara zuwa kasashen duniya.

“Kamfanin yana cika dukkan sharuddan ingancin abinci na hukumomin Indonesiya da sauran ƙasashen da yake hulda da su.”