✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Najeriya ta zama Gwarzuwar Girki ta Duniya

A halin yanzu Hilta ta riga ta haura awa 87 da minti 45 tana girki, kuma burinta shi ne kaiwa awa 96

’Yar Najeria mai shekaru 27, ta kafa tarihin zama wadda ta fi kowa dadewa tana girki a duniya.

Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci ta kafa tarihin ne bayan da ta sha gaban Lata Tondon  ’yar kasar Indiya wadda a shekarar 2019 Kundin Tarihi na Duniya na Guiness ya ba ta kambin.

Lata ta samu kambin ne bayan ta shafe awa 87 da minti 45 tana girki, amma burin Hilda, shi ne kaiwa awa 96 tana yin girkin.

Tuni kuma ta haura awa 88 a girkin nata, wanda ta fara tun da misalin karfe 4 na yammacin ranar Alhamis a Amore Gardens da ke unguwar Lekki a Jihar Legas.

Ana kuma haske girkin nata kai-tsaye a kafar YouTube, kuma tuni fitattun ’yan siyasa da sauran ’yan Najeriya suka fara taya ta murna.