✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yar gwamnan Delta ta kamu da COVID-19, ya killace kansa

Gwamnan Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya killace kansa bayan diyarsa ta kamu da cutar COVID-19 a ranar Juma’a. Nan take bayan gano ‘yar tasu…

Gwamnan Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya killace kansa bayan diyarsa ta kamu da cutar COVID-19 a ranar Juma’a.

Nan take bayan gano ‘yar tasu ta kamu da cutar ne Okowa da matarsa da sauran ‘ya’yansu suka killace kansu sai bayan kwana 14.

Sakataren Yada Labaran gwamnan Olisa Ifeajika, a sanarwa da ya fitar ya kara da kira ga jama’ar jihar da su yi hattara da kamuwa da cutar ta hanyar kiyaye matakan kariya.

Gabanin sanarwar Okowa ya wallafa cewa, “Yau ni da Edith mun samu labarin diyarmu ta kamu da COVID-19. Don haka mu biyun za mu killace kanmu sai bayan kwana 14 kamar yadda dokar ta tanada”.