Wata mata, Shidoo Tortiv da ta tsere daga matsugunninta sanadiyyar matsalar tsaro ta haifi ’yan huɗu a gidan ’yan uwa da take zaman gudun hijira a Jihar Benuwe.
Shidoo Tortiv wadda ta fito daga ƙauyen Ucha na Ƙaramar Hukumar Gwer ta Yamma sun tsere tare da mijinta, Wilfred Tortiv sakamakon matsalar tsaro da ta yi kamari, inda suka nemi mafaka a gidan ’yan uwansu.
- Bom ya kashe masu yawon murnar sallah a Sakkwato
- Isra’ila ta ƙwace jirgin ruwa a hanyar kai agaji Gaza
Mista Wilfred Tortiv Mijin matar ya shaida wa wakilinmu a ranar Litinin cewa ta haifi jariran ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Asabar a gida bayan nakuda ta kama ta kuma ungozomai suka karbi haihuwar saboda babu lokaci da kuma kudin kai ta asibiti.
Ya bayyana cewa wannan ce haihuwa ta uku da matarsa ta yi kuma duk ’ya’yanta na farko da na biyu maza, sai dai wannan da aka samu maza biyu da mata biyu, lamarin da ya ce dawainiyarsu za ta kara musu matsin rayuwa.
Tuni dai Gwamna Hyacinth Alia ya bayar da umarni mika matar da yayan da ta haifa zuwa Asibitin Koyarwa na Jamiar Benuwe da ke Makurdi domin samun kulawar da ta dace.