Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ta ce, yana da muhimmaci a samar da wata ingantacciyar hanyar sanya farashin kayayyakin Intanet da na harkokin data a Najeriya.
Babban Mataimakin Shugaban Hukumar NCC, Farfesa Umar Garba dambatta ya bayyana haka a taron Masu Ruwa-Da-Tsaki kan nazarin samar da farashi kaya da harkokin data a Najeriya da aka gudanar a Legas a makon jiya.
Ya ce, samun wadatattu kuma ingantattun harkokin Intanet ya dogara ne a kan farashin da ake caji a wadannan harkoki, inda ya ce tabbatar da farashin da ake caji ga masu sayar da zangon lokacin sadarwa da data su dace da kudin da duniya ta amince da shi na da muhimmanci wajen isarwa da fara aikin harkokin sadarwar Intanet da na data a Najeriya.
Ya ce babu shakka Masana’antar Sadarwa ta Najeriya ta samu gagarumar bunkasa a ’yan shekarun nan tare da yin tasiri da samar da amfanin da ke zuwa da ci gaba a kowane bangare na tattalin arzikin Najeriya da rayuwar jama’arta.
Ya ce: “Yayin da hukumar take murna da wannan gagarumin ci gaba da aka samu a masana’antar, musamman masu sayen lokacin kira a layukan waya, muna da yakini kashi na gaba zai tabbatar da kowa – a duk inda yake zaune kuma a duk halin da yake ciki – ya samu cin gajiyar sadarwar Intanet da tarho, sai dai hakan zai samu ne idan aka isar da kayayyakin sadarwar Intanet da tarho zuwa sassan kasar nan, bisa lura da muhimmancin sadarwar Intanet a matsayin mabudi ga ingantuwar aiki da bunkasa tattalin arziki da ci gaban kasa da inganta zamantakewar jama’a da musayar al’adu.”
Ya kara da cewa: “Yayin da ake kokarin magance batutuwan babakere a harkokin kasuwanci musamman masu sayen sari suna sayar wa masu amfani da su wata hanya ce ta tsara gasa a matakan farashi ga masu sayen kayayyakin sadawar da Intanet, kuma ta yiwu wannan mataki ba zai wadatar kan magance batun farashin a dukan sassan masu sayarwa ba, ta haka akwai bukatar wasu dokokin da za su dace.”
Domin sauke nauyin da aka dora wa hukumar na samar da kyakkyawan yanayi da karfafa gasar da ta dace a masana’antar sadarwa da kuma cimma manufar shirin Samar da Harkokin Sadarwa na kasa, ya ce, ya zamo wajibi a tsara wata hanyar sanya farashi ga harkokin sadarwa a Najeriya.
“Wannan ba zai tsaya a kan samar da wadatattu da mayalwatan hanyoyin sadarwa kadai ba, zai ma tabbatar da gasa tare da sanya ido kan tauyewa a fannin farashi da tsadar farashi ko farashin yaudara da sauransu,” inji shi.
Ya ce, wannan ya sa yana da muhimmanci a gudanar da nazari kan Tsara Farashin Masu Sayar da lokaci da data a Najeriya. Kuma domin cimma haka hukumar ta gabatar da tsarin gudanar da cikakken bincike inda ta nada Kamfanin kwararru kan Binciken Kudi na KPMG domin gudanar da abubuwan da suka hada da:
* Tsara ka’idoji don daidaita farashi ga masu amfani da lokacin kira a tarho da data a Najeriya musamman yanke shawara kan mafi tsadar farashi da riba a inda ya zama dole;
* Tsara fasalin farashin da ya dace da harkokin kasuwar sadarwa da data a Najeriya tare da lura da yadda ake gudanar da haka a duniya;
* Tsara wata hanya ta karbar bayanan da za a yi amfani da su wajen yanke shawarar;
* Tsara kudin dabarun ingantawa da hanyoyin da za a aiwatar da su;
* Tsara ma’aunan dokokin farashin da ya dace da za a amince da su;
* Tsara bukatar samar da wasu dokoki na yin tara ko hana wuce ka’ida a abin da ya shafi sanya farashi ga masu amfani da lokacin kira da data;
* Samar da ma’anar da ta dace ga manya da sababbin shiga da kananan masu gudanarwa, a idan ya zama tilas;
* A gudanar da cikakken awon ayyukan kasuwanci ga masu amfani da wasu harkokin kasuwancin kayayyakin sadarwa da data domin samar da dabarun da suka dace don amincewa da su; da kuma
* Tsara wani fasalin kudin da ya dace domin tsara farashin sayen hanyoyin sadarwa da data ta yadda za su dace da sassan kananan harkokin tattalin arziki da kimiyya da kere-kere.