✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan wasan Barcelona 10 da suka girgiza duniyar tamaula

Jerin ‘yan wasa 10 da suka yi suna wajen taka leda a Barcelona.

Kulob din Barcelona daya ne daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya, wanda ya samu tarin nasarori a shekaru daban-daban.

Ga jerin ‘yan wasa 10 da suka yi suna wajen taka leda a Barcelona, cikin shekaru 20 da suka wuce, inda kulob din ya ci kofuna da kambuna sakamakon tallafin da wadannan gwarazan ‘yan wasa suka ba shi.

Shafin wasanni na Goal.com ne ya fitar da wannan jeri mai cike da bayanan rawar da kowannensu ya taka wa kulob din na Sifaniya.

Na farko: Lionel Messi

Wa ne idan ba Messi ba? Messi ya nuna wa duniya yadda ake zama gwarzon dan wasa a yayin zamansa a Barcelona, inda ya yi gogayya da Cristiano Ronaldo wajen cin kambun Ballons d’Or guda 12.

Ba za a iya zayyano adadin tarihin da Messi ya goge kuma ya kafa sabo ba a Barcalona. Kyaftin na Argentina ya ci kyautar Takalmin Zinare na Turai sau shida da Ballon d’Or bakwai.

Idan ba don rawar da Messi ya taka mata ba, Barcelona ba za ta iya cin rabin kofunan da ta ci ba a wannan karni.

Tafiyar Messi daga Barca ta girgiza zukata a duniya, inda har yau ake burin dawowarsa don ci gaba daga inda ya tsaya.

Na biyu: Xavi Hernandez

Xavi ya buga wa Barcelona wasa tsawon shekara 17, daga 1998 zuwa 2015. Babu dan wasan Barca da ya buga yawan wasan da Xavi ya buga kungiyar a Turai.

Ya gwanance wajen daga tuta lokacin da ake matukar bukatar wanda zai daga. Hakan ya bayyana lokacin da ya ciyo wa Barca kwallo a wasan karshe na kofin Zakarun Turai na 2011, inda suka doke Manchester United.

Kamar yadda ya saba, Xavi ya mamaye tsakiyar fili a wasan, inda a karshe aka ba shi kyautar gwarzon dan wasa na ranar, har sai da kocin Man U ya yaba masa bayan kare wasan.

Na uku: Andres Iniesta

Iniesta ya samu horo ne a shahararriyar makarantar kwallon kafa ta Barcelona, wato La Masia, kuma gwani ne kan dabarun rike wasa.

Ana shan wahala kafin a karbe kwallo daga hannunsa, inda yakan yi sintiri tsakanin tsakiyar fili da kuma gaba.

Akwai lokuta da dama da Iniesta ya nuna bajinta, amma dai tarihi ba zai manta da wasan dab da na karshe da suka buga da Chelsea ba, a gasar zakarun Turai.

Iniesta ne ya farke wa Barcelona kwallo a karin lokaci a zagaye na biyu na wasan, bayan masoya Chelsea sun yi ta korafin alkalin wasa Tom Henning Ovrebo ya ki ba su bugun durme, a lokuta daban-daban.

Na hudu: Ronaldinho

Babu dan wasan Barca kamar Ronaldinho wajen nuna bajinta a wannan karni na 21. Wasansa na farko a Barca wani batu ne da ake yawan maimata shi a tarihi, saboda kyan cin kwallo da ya yi a wasan.

An fara wasan ne sha biyun dare, sakamakon cewa Sevilla ta nemi a buga wasan ranar Laraba, bisa tunanin Ronaldinho ba zai samu zuwa ba, saboda zai tafi buga wa kasarsa Brazil wasa.

Barcelona ta amince da bukatar Sevilla, amma sai ta yi kokari wasan ya zama na farko da aka buga a ranar, wato agogo yana buga shabiyun dare.

Gwanintar iya yanka da Ronaldinho ya nuna a wasan nan, shi ya kayatar da ‘yan kallo kimanin 80,000 da suka cika sitadiyam din.

Bayan dan, Ronaldinho ya taka rawar gani sosai tsawon zamansa a Barca, inda ya taimaka wajen ciyo kofuna masu yawa.

Na biyar: Sergio Busquets

An haifi Sergio Busquets a Catalunya kuma babansa ma ya buga wa Barca wasa. Busquets ya sanar a watan Mayun nan, cewa zai bar kulob din a karshen kakar bana ta 2022-23, bayan zamowa na uku a jerin wadanda suka fi kowa yawan wasanni a Barcelona.

Cikin shekara 18 da ya taka leda a Camp Nou, Busquets ya ci duka kofunan da yake da damar ci yayin zamansa a Barca.

Kofunan sun hada da La Liga takwas, da Copa del Rey bakwai, da na Zakarun Turai guda uku, da Kofin Duniya na Kulob guda uku. Haka nan, Busquets zai bar Barcelona ne bayan ya daga kofin Laliga na tara.

Duk da koci Xavi ya so Busquets ya tsawaita zamansa a Barcelona, dan wasan ya zabi tafiya, inda ake hasashen zai koma gasar MLS ta Amurka, ko gasar Saudi Pro ta Saudiyya.

Na shida: Luis Suarez

Barcelona sun ci burin sayo Suarez a shekarar 2014 inda suka janyo ya zama daya daga cikin ‘yan wasa mafi tsada da aka saya a duniya lokacin da ya baro Liverpool.

Kamar yadda ya saba, zuwan Suarez ke da wuya, sai ya ciji dan wasa Giorgio Chiellini a gasar Kofin Duniya, inda aka dakatar da shi daga buga kwallo na wani lokaci.

Bayan kammala wa’adin dakatarwar, Suarez ya fara buga wa Barca wasa a karawarsu da Real Madrid inda suka sha kaye. Amma Suarez ya taka rawa, inda ya taimaka wa Neymar cin kwallon farko cikin minti hudu da fara wasa.

Suarez da Neymar da Messi su ne suka yi kaurin suna a matsayin dodanni uku da ake wa lakabi da MSN, wato Messi-Suarez-Neymar.

An ji takaicin barin Suarez Barca, inda ya koma Atletico Madrid kuma ya ciyo wa sabon kulob din nasa kofin La Liga a shakararsa ta farko.

Na bakwai: Samuel Eto’o

Samuel Eto’o ya taba ikirarin cewa shi ne dan wasan da ya fi kowa kwallon kafa a Afirka a tarihi, duk kuwa da cewa akwai irin su Didier Drogba da za su iya yin wannan ikirari.

Eto’o ya ce a shekarar 2020, “Babu daya cikin sauran ‘yan wasan Afirka da zai zo ya ce ya kai ni, ko ya fi ni.”

Ya kara da cewa, “Ba wai ni ne na fada ba, da ma haka ne gaskiyar lamarin, kowa ya sani. Na yi burin zama gwarzon da ya fi kowa, kuma hakan ce ta faru, ni ne na daya lokacin da ina buga wasa.”

Baya ga zamowa na daya a nahiyarsa, Samuel Eto’o yana cikin jigajigan ‘yan wasan da suka bugawa Barcelona a tarihi.

Ya ci kwallaye 130 a wasannin 199 kacal. Wannan ya ishi yin kuri, kuma an yi kewarsa lokacin da Barca ta sallame shi, don ta kawo dan wasan nan Zlatan Ibrahimovic a shekarar 2009.

Yayin da Ibrahimovic ya yi ta faman rikici da kocin Barca, Guardiola, shi kuwa Eto’o yana can a Inter Milan inda ya taimaka musu suka ci kofuna uku a shekarar.

Ba za a manta da tasirin Eto’o a wasan da Inter suka buga da Barca ba, a matakin dab da na karshe a gasar zakarun Turai ta shekarar ta 2010.

Na takwas: Dani Alves

Dani Alves ya buga wa Barca wasa a karo biyu, na farko a tsakanin 2008 da 2016, inda ya zamo daya daga cikin gwarazan ‘yan wasan gaba da aka taba gani.

Dan asalin kasar Brazil, Alves ya taimaka wa Messi wajen nasarorin cin kwallaya, sakamakon taka rawa irin ta dan wasan gefe mai kwazo.

Alves ya dawo Barca a watan Janairun 2022, inda ya amince da karbar mafi karancin albashi da ya taba karba a kulob din.

Na tara: Carles Puyol

Shi ma Puyol ya samu horo a makarantar nan ta La Masia, kuma baya ga suna da ya yi saboda gashin kansa mai buzu-buzu, ya kasance gwanin dan wasan baya.

Bayan ya yi fice har ya samu shiga sahun farko na ‘yan wasan 11 da ake zaba a shekarar 2000, Puyol ya taka rawa duk da lokacin Barca ba ta zamo abar tsaro ba irin na shekarun dab da 2010.

Puyol ya yi ritaya a shekarar 2014, inda aka ruwaito shi yana cewa, “Na cimma nasarorin da dubunnan yara a duniya suke mafarkin cimmawa. Na yi sa’a a rayuwa. Na zo nan ina yaro, amma yanzu zan tafi ina da iyalai.”

Na goma: Gerard Pique

Gerard Pique dan wasan baya na Barca ne, kuma an haife shi ne a cikin dangin da ke matukar kishin Barcelona, kuma a baya kakansa ma ya taba zama mataimakin shugaban kulob din.

Alakar Pique da Barcelona ta kai matsayin da bai iya jure zama Manchester United inda ya fara buga wasa ba a 2004, inda ya koma gida Camp Nou a shekarar 2008.

Dawowarsa ke da wuya, sai Pep Guardiola ya jagoranci Barcelona suka ci kofuna uku a shekarar. A duka wasannin kulob din, da wuya ka ga ba a saka Pique ba.

Pique ya bugawa Barca wasa har shekarar bara, 2022, inda ya ciyo wa kulob din kofuna masu tarin yawa.

Lokacin da tsufa ya fara cimma sa, bai daina dagewa wajen tallafawa kulob din nasa ba. Hakan ya bayyana lokacin da ya amincewa da ragin albashi, yayin da kulob din ya shiga matsalar kudi.

Don haka ba za a yi mamaki ba idan Gerard Pique wata rana ya zamo shugaban kulob din mai matukar tarihi.