✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan wasa 11 da za su yi takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan FIFA na 2021

A bangaren masu horaswa kuma, FIFA ta fidda sunayen mutum bakwai da za su yi takara.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), ta bayyana sunayen ’yan wasa 11 da za su yi takarar lashe kyautar gwarzon dan wasa na bana.

Aminiya ta ruwaito cewa, cikin jerin sunayen ’yan wasan da FIFA ta fitar da za su yi takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara, dukkansu suna taka leda ne a manyan kungiyoyin kwallon kafa na nahiyyar Turai.

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi na cikin jerin ’yan wasan da za su yi takara kamar yadda suka saba tun bayan da aka kaddamar da bayar da kyautar a shekarar 2016.

Hukumar FIFA wadda ta fitar da sunayen ’yan wasan, ta ce za a bayyana gwarzon bana a wani kwarkwaryar biki da za a gudanar a ranar 17 ga watan Janairun 2022.

Sanarwar da FIFA ta fitar a shafinta, ta ce za a ci gaba tattara kuri’u daga kyaftin din tawagun kasashe da masu horaswa, magoya baya da kafafen yada labarai na duniya har zuwa ranar 10 ga watan Dasumba na 2021.

Sai dai FIFA ta ce bikin bayar da kyautar da za a gudanar a Hedikwatarta da ke birnin Zurich na kasar Switzerland, zai gudana ne kai tsaye ta Intanet saboda annobar Coronavirus.

Dan wasan Bayern Munich da tawagar Poland, Robert Lewandowski ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na FIFA a bara.

A wancan lokaci, Lewandowski wanda ya yi takara tare da Cristiano Ronaldo da kuma Lionel Messi, ya ci kwallaye 35 a wasa 47 da hakan ya taimaka wa Bayern Munich lashe kofi uku.

Gwarazan ’yan wasan da FIFA ta fitar sun hada da:

  • Karim Benzema (France / Real Madrid CF)

  • Kevin De Bruyne (Belgium / Manchester City FC)

  • Cristiano Ronaldo (Portugal / Juventus FC / Manchester United FC)

  • Erling Haaland (Norway / BV Borussia 09 Dortmund)

  • Jorginho (Italy / Chelsea FC)

  • N’Golo Kanté (France / Chelsea FC)

  • Robert Lewandowski (Poland / FC Bayern München)

  • Kylian Mbappé (France / Paris Saint-Germain)

  • Lionel Messi (Argentina / FC Barcelona / Paris Saint-Germain)

  • Neymar (Brazil / Paris Saint-Germain)

  • Mohamed Salah (Egypt / Liverpool FC)

A bana dai babu masu tsaron gida a cikin jerin wadanda za a zabi zakara domin lashe kyautar gwarzon dan wasan FIFA na shekara, duk da cewa masu tsaron gida suna da tasu kyautar.

Gianluigi Donnarumma na Italiya, wanda aka zaba a matsayin gwarzon dan wasa a gasar EURO 2020, yana daga cikin ’yan takarar masu tsaron gida biyar da suka hada da:

  • Alisson Becker (Brazil / Liverpool FC)

  • Gianluigi Donnarumma (Italy / AC Milan / Paris Saint-Germain)

  • Édouard Mendy (Senegal / Chelsea FC)

  • Manuel Neuer (Germany / FC Bayern München)

  • Kasper Schmeichel (Denmark / Leicester City FC)

A bangaren masu horaswa kuma, FIFA ta fidda sunayen mutum bakwai da za su yi takarar lashe kyautar gwarzon mai horaswa na bana. Sun hadar da:

  • Antonio Conte (Italy / FC Internazionale Milano / Tottenham Hotspur FC)

  • Hansi Flick (Germany / FC Bayern München / German national team)

  • Pep Guardiola (Spain / Manchester City FC)

  • Roberto Mancini (Italy / Italian national team)

  • Lionel Sebastián Scaloni (Argentina / Argentinian national team)

  • Diego Simeone (Argentina / Atlético de Madrid)

  • Thomas Tuchel (Germany / Chelsea FC)