✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan uwan Gwamnan Sakkwato sun sauya sheka daga jam’iyyarsa

Shugaban APC na Jihar Sakkwato, Isah Sadik Acida, ya tabbatar wa wakilinmu sauya shekar ’yan uwan gwamnan — Alhaji Kabiru Moyi da Habibu Waziri Tambuwal…

Yaya da kanen Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal sun suya sheka daga jam’iyarsa ta PDP zuwa APC tare da Almajiran Zawiyyar da ke cikin garin Tambuwal.

Shugaban APC na Jihar Sakkwato, Isah Sadik Acida, ya tabbatar wa wakilinmu sauya shekar ’yan uwan gwamnan — Alhaji Kabiru Moyi da Habibu Waziri Tambuwal — zuwa jam’iyar.

Ya ce, “Kabiru Moyi sama da shekara daya muna huldar siyasa da shi da kaina na kai shi gidan Sarkin Yamma, tun a lokacin yake tare da mu, ganin su da ka yi tare da dan takarar gwamnanmu magana ce ta siyasa sun dawo jam’iyarmu ta APC.”

Tun bayan bullar hotunan ’yan uwan gwamnan, tare da dan takarar gwamnan jihar na Jam’iyar APC ya haifar da rade-radin fitar su daga PDP.

Wani makusantan Kabiru Moyi ya ce yana ganin ya bar PDP ne domin Gwamna bai taimake shi ba.

Fitar Habibu Waziri tafi ban mamaki, saboda makusanci ne ga Tambuwal, Babban Darakta ne a gwamnati, kuma dan wa da kane suke da Gwamna Tambuwal — amma ya jefar da tafiyar siyasar dan uwansa nasa.

Sauyin shekar tasa ta sanya almajiran Zawiyyarsu suka bi shi zuwa APC dukansu kamar yadda wata majiyar ta tabbatar.

Yunkurin jin ta bakin Kabiru da Habibu kan dalilansu na sauya sheka lamarin ya ci tura.