✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan ta’adda sun kashe masu neman mafaka a Dimokuradiyyar Kongo

’Yan ta'addar sun hallaka sama da mutum 18 da ke neman mafaka a yankin.

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokiradiyar Kongo sun tabbatar da kisan fararen hula 18 da wata kungiyar ’yan ta’adda ta aikata a hari wani coci da mutanen da suka rasa matsugunansu ke zaman mafaka a yankin Djugu.

Wani jami’in majami’ar Katolika da ke kauyen Kilo a yankin Ituri, ya ce an kai musu harin ne da misalin 5.30 na safiya, lokacin da ’yan ta’addar suka bude wuta a ginin da ke dauke da mutane kusan 1,000.

Jean-Pierre Basiloko, da ke wakiltar shugabannin kungiyoyin kwadago a yankin ya ce sai da ’yan ta’addar suka fara kai hari a kan sansanin sojin da ke yankin kafin su afka wa mutanen da suka rasa matsuguninsu.

Ana danganta maharan da kungiyar CODECO wadda ke ikirarin neman ci gaban ’yan kabilar Lendu  da ke gaba da ’yan kabilar Hema.

Rikicin kabilun ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga 1999 zuwa 2003, kafin daga bisani a girke dakarun samar da zaman lafiya daga kungiyar Tarayyar Yurai a yankin.

Kungiyar agaji ta kasar Denmark ta ce hare-haren da kungiyar CODECO ke kaiwa sun  yi sanadiyar hallaka dubban mutane da kuma tilasta wa sama da miliyan 1.5 barin gidajensu, yayin da sama da rabin mutanen yankin ke fama da matsalar karancin abinci.

A ranar 16 ga watan Fabrairu, kungiyar ta yi garkuwa da mutum takwas ciki har da wani Janar na sojin da Shugaba Felix Tshisekedi ya tura don jagorantar taron zaman lafiya a yankin.