✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun kashe fararen hula 30 a Mali

Maharan sun tare motar fararen hula suka kashe mutum 31 tare da jikkata wasu 17

Matafiya fararen hula akalla 30 ne ’yan ta’adda suka hallaka a garin Mopti na kasar Mali.

Gwamnatin kasar ta ce mutum 31 ne aka kashe, aka kuma jikkata wasu 17 a harin da aka tare motar matafiyan.

Wani jami’in gwamnati ya ce wadanda aka kashe din sun hada da mata da kananan yara kuma “An yi wa fasinjojin ruwan wuta ne sannan aka banka wa motarsu wuta

“Amma an tura jami’an tsaro zuwa yankin,” da ke kusa da garin Bandiagara, kamar yadda ya shaida wa kamfanin daillancin labarai na AFP.

Maharan sun tare fararen hular ce a ranar Juma’a suka bude musu wuta, amma kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin.

Tun a shekarar 2012 kasar Mali ke fama da yaki da masu tayar da kayar baya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro da fararen hula da dama.

Duk da girke dakarun kasar Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya a kasar, ayyukan masu tayar da kayar bayan na ci gaba a kasar tare da yaduwa a makwabtanta da suka hada da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.

Rikicin na Mali ya fi kamari a yakin Tsakiyar kasar inda ake yawan kai wa sojoji hare-hare.