✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sintiri sun kashe masu garkuwa da mutane

‘Yan sintiri sun kashe masu garkuwa da mutane guda uku suka kama ‘yan leken asirin bata-garin guda biyu a Jihar Kogi. Tawagar tsaron a Kananan…

‘Yan sintiri sun kashe masu garkuwa da mutane guda uku suka kama ‘yan leken asirin bata-garin guda biyu a Jihar Kogi.

Tawagar tsaron a Kananan Hukumomin Adabi da Okehi sun dirar wa ‘yan jihar ne a sa’ilin da suke shirin tare babbar titin Lokoja zuwa Okene, titin da a karshen makon jiya aka sace da matar tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo, Hassan Zakawanu, a ranar rasuwarsa.

Tawagar da ta kunshi ‘yan banga da mafarauta da ‘yan sanda, ta kuma damke ‘yan leken asiri biyu na masu garkuwan da suka ce su ke sanar da su motsin matafiya a kan titin.

Babban Mai ba Gwamna Yahaya Bello Shawara kan Tsaro a Karama Hukumar Okehi, Abdulraheem Ohiare, ya ce takwaransa na Adavi, Joseph Omuya Salami ne ya jagoranci zuwa maboyar masu garkuwa da mutanen.

Ya ce da ganin su sai masu garkuwar suka bude musu wuta, amma bayan musayar wuta, sun kashe uku da cikinsu miyagun, wasu da suka samu raunin bindiga kuma suka sha da kyar.

Ya ce an kwaci manyan bindigogi albarusai da abin rufe fuska da layu a hannun miyagun.