✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sandan Isra’ila sun fatattaki Musulmi masu ibada a masallacin birnin Kudus

Kusan duk watan azumi sai Isra'ila ta kai makamancin wannan harin

A karo na biyu cikin kwana biyu, ’yan sandan Isra’ila sun yi amfani da harsashin roba da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa Musulmai masu ibada a watan azumin Ramadan

Gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito cewa yanzu haka Isra’ila ta kori kowa daga ciki masallacin kuma babu kowa a cikinsa.

Bisa al’ada dai, a kowanne watan azumi, Musulmi kan kwana a masallacin domin yin ibadar itikafi.

Yayin farmakin dai, ’yan sandan sun yi wa masallacin kawanya inda suka rika kai hari kan Musulman masu ibada a ciki.

Wasu faya-fayan bidiyo dai sun bulla inda suke nuna yadda ‘yan sandan Isra’ilar sanye da kayan fada da kuma makamai, suka kutsa kai cikin masallacin suna dukan masu ibada, cikinsu har da mata.

A wani labarin kuma, gwamman Yahudawan Isra’ilar ne suka shiga harabar masallacin da sanyin safiyar Alhamis bisa kariyar ’yan sandansu.

Ko da sanyin safiyar ta Alhamis dai sai da ’yan sandan suka hana Musulmai shiga ciki domin gudanar da sallar Asuba a ciki, inda hakan ya tilasta musu yin sallar a waje.

Kusan tsawon shekaru ke nan