✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sandan da ke karbar na-goro sun ba ni kunya —Alkali Baba

Ya bayyana takaici kan yadda aka samu wasu jami'ai suna muzguna wa jama'a.

Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya bayyana cewa jami’an da ke karbar na-goro sun ba shi kunya.

Alkali Baba ya bayyana takaicinsa kan yadda aka samu wasu jami’an ‘yan sanda da muzguna wa jama’a, musamman masu karbar na-goro.

Don haka ya bukaci dukkan Kwamishinoni da Kwamandojin ‘yan sanda da su mai da hankali sosai wajen sanya wa jami’ansu ido yadda ya kamata.

A cewar Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda, CSP Olumuyiwa Adejobi, Baba ya yi gargadin rundunar ba za ta lamunci halin muzgunawa da kuma karbe sulalan jama’a da wasu jama’ai ke yi ba.

Kazalika, ya bai wa Maitaimakin Sufeto-Janar (AIG) na sashen tattara bayanan sirri, umarnin sanya ido kan wasu rassa uku na rundunar wajen tabbatar da suna aikinsu yadda ya kamata ba tare da take hakkin jama’a ba.

Ya ce an dauki wannan mataki ne domin tabbatar da sassan rundunan sun cimma manufofinsu na aiki.

Rahotanni sun ce Alkali Baba ya ba da sanarwar korar Liyomo Okoi, wani jami’in dan sanda mai mukamin Kwanstebul da lambar aiki 524503.

Sanarwar ta ce an kori Okoi da ke Ofishin Ekori a Kuros Riba, daga aiki bayan da aka kama shi da rashin da’a kamar yadda wani bidiyonsa da aka nada ya nuna.